Mutane 28 sun hallaka a wani harin kudancin Kaduna

0
192

A daren lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a ƙauyukan Malagum 1 da Sokwong da ke masarautar Gworok a ƙaramar hukumar ƙaura a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane kusan 28 tare da jikkata wasu da dama.

Da yake tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, Sakataren majalisar ƙaramar hukumar Kaura, Hon. Raymond Ibrahim ya ce ‘yan bindigar sun fara kai hari a yankin Sakwong ne da misalin ƙarfe 11:58 na dare, inda suka kashe mutane 9 tare da ƙona gidaje da ƙadarori.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun ƙona wani tsoho ɗan shekara 90 har lahira, sun kuma raunata mutum 3 a Gombe

“Mun je wurin da lamarin ya faru a safiyar yau, sai muka ga gawarwaki tara da idanunmu, daga nan ne muka je Malagum ta ɗaya inda muka tabbatar daga wata majiya cewa an kashe mutane 19 a can,” inji shi.

Ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyar kaɗan bayan an kai hari a Malagum ta ɗaya inda aka kashe mutane hudu, inda yayi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu.

Hon. Ibrahim yayi ƙira ga gwamnati da ta taimaka wa jama’arsu domin da yawa daga cikinsu sun rasa matsugunansu.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jamhuriyar har Kaduna DSP Muhammed Jalige, bai amsa kiran waya ba.

Leave a Reply