Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kama wata matar ‘yar shekara 52, Misis Bose Adegoke tare da ɗiyarta ‘yar shekara 28, Misis Yetunde Adegoke bisa zargin kashe wani matashi ɗan shekara 25 (wanda aka sakaye sunansa) lamarin da ya abku a garin Iseyin da ke ƙaramar hukumar Iseyin, a jihar.
Waɗanda ake zargin, an kamosu ne a wurare daban-daban, a halin yanzu suna hannun hukumar binciken manyan laifuka ta jihar, da ke Iyaganku a Ibadan domin yi musu tambayoyi.
Binciken ya nuna cewa matashin wanda a baya yake zaune tare da mahaifiyarsa, kwatsam ya watsar da ita kuma ya tattara kayansa a asirce ya koma gidan Adegoke kafin lamarin ya faru.
Wata majiyar ‘yan sanda ta ce, “Wanda aka kashe da Yetunde suna soyayya, Yetunde nada ‘ya’ya biyu yayin da shi wanda aka kashe ba shi da ko ɗa ɗaya, kasancewarsa matashi mai shekaru 25, suna cikin soyayya mai tsanani kuma Yetunde ta sanar da mahaifiyarta game da dangantakar kuma mahaifiyarta ta amince, haka suka yaudari matashin kan ya dawo gidansu, kuma ya amince.
“Ya shafe watanni yana tare da su a Ibadan, bayan da suka gano cewa mahaifiyarsa ta damu, sai suka nema masa ɗaki a garinsu Iseyin inda ya zauna kusan wata biyar kafin ya kamu da rashin lafiyar da tayi ajalinsa.
“mahaifiyar sa ta damu da halin da ake ciki, sai ta kai ƙara ofishin ‘yan sanda na Gbagi, reshen Egbeda a Ibadan, kuma ‘yan sanda sun samu nasarar gano shi a wurin mahaifiyar Yetunde a Ibadan amma ya shaida wa ‘yan sanda cewa ba ya son ya koma gurin mahaifiyarsa, hakan ya sa Yetunde da mahaifiyarta suka mayar da shi gidansu da ke Iseyin, suka samar masa aikin hannu.
Bayan ‘yan makwanni, mahaifiyar Yetunde wacce ma’aikaciyar gwamnati ce ita ma ta koma daga Ibadan zuwa Iseyin kuma suna kwana a ɗaki daya da yaron da.
“Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce matashin kafin mutuwarsa ya furta cewa mahaifiyar budurwar tasa tana tursasa shi yayi lalata da ita, inda take yi masa fyaɗe.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Lokacin da ya yi rashin lafiya, sai suka garzaya da shi wani asibiti a Iseyin, suka bar shi a can, amma da bai sami sauƙi ba, mahukuntan asibitin sun samu damar kiran mahaifiyarsa da ta je Iseyin ta dawo da shi Ibadan domin kula da lafiyarsa, inda da aga ƙarshe ya mutu bayan ‘yan kwanaki.
” Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, duk kokarin neman jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Adewale Osifeso, domin jin ta bakinsa, bai yi nasara ba.
[…] KU KUMA KARANTA:Yan sanda sun kama uwa da ‘yarta bisa zargin kisan saurayinsu […]