Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA

3
562

Hukumar kula da iyakokin ruwan Najeriya (NIMASA) ta samu lambar yabo na girmamawa daga cibiyar ƙwararru akan harkar haraji, inda shima Shugaban hukumar ya samu lambar yabo daga cibiyar a wajen taron liyafar cin abincin daren da ya gudana a birnin Legas.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai yace hukumar NIMASA ta samu lambar yabon ne a ƙoƙarin ta na kiyaye dokokin da suka shafi biyan haraji da ayyukan jinƙai da hukumar ke yi a fadin Najeriya da kuma bada gudunmawar kayayyakin aiki da nufin inganta rayuwar masu ƙananan sana’o’in don habbaka tattalin arzikin Ƙasa.

A ɗaya bangaren, Shugaban hukumar ta NIMASA, Dokta Bashir Yusuf Jamo, ya samu lambar yabo ne a ƙoƙarin shi na tabbatar da ayyukan hukumar sun tafi daidai da na zamani.

KU KUMA KARANTA: Ana tsaka da Sallah ‘yan bindiga sun kashe Liman, sunyi garkuwa da masallata a Katsina

“Idan ba a manta ba, Bashir Yusuf Jamoh ya samu lambobin yabo da dama da suka hada da babbar lambar yabo ta ƙasa wato (OFR) wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi a kwanankin baya,har ila yau, Dr Jamoh ya lashe lambar yabo a Shugabanci na Zik”.

“Ita da wannan lambar yabo da cibiyar kwararru akan harkar haraji ta baiwa Bashir Jamoh ita ce ta baya bayan nan a ƙoƙarin shi wajen ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba” inji sanarwar.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here