Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba da safiyar Juma’a, sun kai hari a wani masallaci da ke Ughelli a jihar Delta, inda wasu masallata 11 suka jikkata.
Wani mazaunin garin da ya zanta da kamfanin dullancin labarai na Najeriya (NAN) ta wayar tarho, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:47 na safe a lokacin da wasu mabiya addinin Musulunci ke gudanar da sallar asuba a babban masallacin Juma’a da ke kan titin Okoroda a Ughelli.
Mazaunin wanda ya bayyana sunansa da Larry, ya ce da yawa daga cikin mazauna wurin sun farka daga barci sakamakon harbin bindiga da kuma ihun kukan mutanen da ke cikin masallacin.
“Sunana Larry, ni direban abin hawa ne a nan Ughelli. Ina zaune kusa da babban masallacin cikin gari, don haka a safiyar yau da misalin ƙarfe 6:45 na safe muka ji ana harbe harbe a masallacin.
“Saboda tsoro, mutane da yawa a cikin harabar gidana sun firgita kuma mun maƙale a cikin gida mun leƙo domin ganin abin da ke faruwa ta tagogin mu.
“Yayin da harbin ya ci gaba, mun ji kuka mai karfi daga wasu masu ibada a cikin masallacin,” in ji Mista Larry.
A cewarsa, bayan da maharan suka fita, da yawan mazauna garin sun yi dafifi zuwa masallacin domin ganin abin da ya faru. Ya ce mazauna yankin sun taimaka wajen kwashe waɗanda suka jikkata, ya kuma ce waɗanda suka tsira daga harin sun samu munanan raunuka.
Mista Larry ya ce wasu daga cikin masu ibadar sun shaida wa mazauna garin cewa ‘yan bindigar sun tafi da wasu ‘yan uwansu guda uku. Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da harin, sai dai ya ce masallata 11 ne kawai suka jikkata a harin, bai kuma tabbatar da sace wasu masu ibada ba a masallacin.
“Na kira DPO a Ughelli, ya tabbatar min da cewa mutane 11 sun jikkata a harin da aka kai a masallacin.
“Duk da haka, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin, kuma za mu sanar da ku yayin da muke kokarin bankado masu laifin.
“A yanzu, ba a kama kowa akan harinba amma ina tabbatar muku cewa za mu kamo waɗanda keda hannu a harin” in ji Mista Edafe.
[…] KU KUMA KARANTA: Harin ‘yan bindiga a Masallaci ya jikkata mutane da dama a Delta […]
[…] KU KUMA KARANTA:Harin ‘yan bindiga a Masallaci ya jikkata mutane da dama a Delta […]