Mata uwayen alƙawari: Tsawon shekara 39 tana jinyar mijinta bata gujeshi ba

0
558

Bernadette Adams, ta cancanci duk shekara a bata lambar girmawa ta “TANTABARA UWAR ALƘAWARI.” Sun yi aure tun a 1969, tana da shekaru 24, shi kuma yana ɗan 19. Shekarunsu 52 da aure.

Mijinta, Jean-Pierre, ɗan ƙwallon ƙwafa ne a Faransa a kulob ɗin PSG. Har ana masa kirari da “dutse” saboda hana abokan wasa jefa ƙwallo a raga.

Asalin ciwonsa, ya ɗan ji ciwo ne a guiwarsa, daga kaishi asibiti yi masa aiki, aka samu kuskure aka masa allurar kashe jiki. Tunda yayi bacci daga aikin nan bai ƙara farkawa ba, ya na bacci tsawon shekara 39, har zuwa lokacin mutuwarsa a 6 September 2021.

Wannan mata tayi riƙon amana sosai;
Ga ta fara,
gashi ɗan Africa.
Ga ta ƴar asalin Faransa,
shi kuma daga ‘yan gudun-hijira yake,
amma a haka ta aureshi, duk da ta fishi komai.

Daga cikin abubuwan alfahari da ta yi gameda riƙon amana:
Tun da ya samu matsala bata rabu da shi ba har ya mutu.
Bata auri wani ba, kuma bata taɓa sanyawa a ranta zata auri wani ba, alhali ga mijinta baya hayyacinsa.
Ita ke kula da shi tsawon shekara 39.
Ta sha zuwa filin ƙwallo don tunawa da zamanin da suke soyayya a baya.
An so a yi masa allurar mutuwa domin ya huta itama ta huta amma taƙi yarda.
Lokacin da mijinta na asibiti, kullum sai ta yi abinci ta kai masa.

Leave a Reply