A watan Disamba Hukumar Alhazai zata fitar da adadin mutanen da za suyi aikin Hajjin 2023 a Najeriya

1
259

Shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa a Najeriya, Zikrullah Kunle Hassan, ya ce a cikin watan Disamba za su fitar da adadin mutanen da za su je aikin hajjin baɗi a faɗin ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a wani taro kan shirye-shiren hajjin baɗi.

Ya ce ba kamar bara ba da aka fuskanci jinkiri ba, a wannan lokaci hukumomin Saudiyya za su tuntuɓesu a kan lokaci domin ba su wadatacen lokacin shirye-shirye.

Ya kuma bayyana yadda matsalar jinkirin inda a wani lokaci ke zama ƙalubale ga shirye-shiryen hukumar.

1 COMMENT

Leave a Reply