El-Rufai ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar bunkasa harkar fim a jihar Kaduna

0
281

Gwamnatin jihar Kaduna ta rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya don bunƙasa wani ƙauye mai suna Film Village a jihar wanda zai samar da guraben aikin yi ga haziƙan masu fasaha, ’yan wasa da masu ɗaukar fina-finai.

Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya gudana ne a babban taron tattalin arziƙi da zuba jari na Kaduna da ake yi, wanda Muhammad Hafiz Bayero mai kula da babban birnin Kaduna da ƙungiyar ‘yan kasuwa da ma’adanai da noma ta jihar Kaduna ne suka gabatar da shi domin kafa ƙauyen fina-finai a rukunin kasuwanci na Kaduna.

Ibrahim Mandawari

A cewar PWC duniyar nishaɗantarwa da hangen nesa na 2020 zuwa 2024, “Kafofin watsa labarai da masana’antar nishaɗin Najeriya na ɗaya daga cikin masana’antar ƙere ƙere da ke haɓaka cikin sauri a duniya, tana da yuwuwar zama mafi girman fitar da ƙasar zuwa ketare tare da hasashen haɓakar kashi 8.6% a kowace shekara, da adadin girma na shekara-shekara na 19.3″.

Ƙauyen fim ɗin idan an kammala shi zai samar da guraben aikin yi ga ‘yan Kannywood da ke gudanar da sana’ar a jihar tare da horar da masu fasahar fasahar fina-finai na zamani.

A kwanakin baya ne wata kaƙƙarfar tawaga daga masana’antar Kannywood da ke Kano ta ziyarci Gwamnan a Kaduna inda suka yi kira da a ƙulla alaƙa tsakanin masana’antar da gwamnatin jihar Kaduna, abin takaici ne a cewarsu ƙauyen fim na naira biliyan 3 da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya baiwa jihar Kano, be kankama ba saboda rashin amincewa da Malaman Musulunci sukayi.

Da yake jawabi a madadin tawagar Alhaji Ibrahim Mandawari, ɗaya daga cikin jiga-jigan masana’antar Kannywood ya shaida wa Gwamnan cewa, dubban matasa da tsofaffi a Arewa sun dogara ne kan kayayyakin da masana’antar ke samarwa don samun abin dogaro da kai. Ya ƙara da cewa sana’ar ta daina zama wata sana’a ta banza, ko gidan masu shaye-shayen miyagun kwayoyi ko masu shaye-shaye, yanzu haka suna da masu digidigirin digirgir (Ph.D) da Digiri na biyu da sauran manyan kamfanoni masu zuba jari a masana’antar, don haka suke son Gwamna ya kafa kauyen fim a Kaduna, hedkwatar Arewacin Najeriya.

Da yake mayar da martani, Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yana sane da dimbin guraben ayyukan yi da masana’antar ta samar wa jama’a don samun abin dogaro da kai, haka nan, yana sane da irin gudunmawar da ‘yan Kannywood suka bayar a zaɓukan 2015 da 2019, sosai.

Nan ba da daɗewa ba, ya yi nuni da cewa, zai kai su ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa ta kut-da-kut don haka za a taimaka musu ta hanyoyi da dama domin bunƙasa ayyukan masana’antar. “Ina sane da ayyukanku kuma nan ba da daɗewa ba, gwamnatina za ta kafa wani ƙauye na fim, a kasuwar baje kolin kasuwanci ta Kaduna da ke Rigachukun tare da samar masa da kayan aiki na zamani da za su taimaka wa ’yan Kannywood a arewacin ƙasar.

Ali Nuhu

A ciki har da horar da wasu masu fasaha daga sassa da dama na ƙasar nan da kuma samar da kuɗaɗen shiga ga jihar, aikin zai kasance da studio na ƙasa da ƙasa, kasuwannin ƙasa da ƙasa, wurin shaƙatawa na ƙasa da ƙasa, ofishin ‘yan sanda, da sauran ayyuka da dama waɗanda za su samar da ayyukan yi ga jama’armu”.

Leave a Reply