Wata mata ta kashe saurayinta a Otel a Nasarawa

2
371

An kama wata mata da ake zargin ta kashe saurayinta a wani Otel a Nasarawa. Matar, mai suna Alice Mulak ta kashe saurayinta a otal din City Rock da ke Unguwan Gwari Marababa, ƙaramar hukumar Karu a Nasarawa da safiyar Juma’a. DSP Ramhan Nansel, Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan ya tabbatar da faruwar lamarin.

Wata mata Alice Mulak ‘F’ ‘yar Ungwan Gwari, ƙaramar hukumar Karu saboda ta kashe saurayinta da wuka. “Jami’an ‘yan sanda da ke aiki da sashin Mararaba ‘A’ a jihar Nasarawa ƙarƙashin jagorancin CSP Musa Babayola sun kama wata Alice Mulak ‘F’ mai unguwar Ungwan Gwari, ƙaramar hukumar Karu bisa laifin kashe saurayin nata da wuka.

“Bincike na farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne a bayan Otel ɗin City Rock da ke Mararaba da misalin karfe 0330 na safe a lokacin da marigayin da budurwarsa suka fara faɗa da juna kashi a sakamakon rashin fahimtar juna.” Yace.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin kuma an gano wuƙar da aka yi amfani da shi wajen aikata laifin bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda, CP Adesina Soyemi. Ramhan Nansel ya ce an miƙa wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Lafia don ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

2 COMMENTS

Leave a Reply