Kamfanin Microsoft zai horas da ƴan Najeriya miliyan biyar

Najeriya da kamfanin fasahar zamani na Microsoft sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar bayar da horo ga mutanen ƙasar miliyan biyar.

A jiya Laraba ne ministan harkokin sadarwa da fasahar zamani na Najeriya, Isa Ali Pantami ya jagoraci tawagar ƙasar wurin sanya hannu kan yarjejeniyar, a Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Najeriya na sa ran matakin zai taimaka wurin ƙarfafa ƙwarewar matasa kan harkar sadarwa ta zamani, da samar da guraben aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Ministan ya shaida wa BBC cewar ana sa ran fara aiwatar da shirin nan ba da daɗewa ba, kuma za a gudanar da shi ne na tsawon shekara biyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *