‘Yan ta’adda sunyi barazanar aure ‘ya’yan tsohon jami’in Zamfara da aka sace

0
261

‘Yan ta’adda sun fitar da wani faifan bidiyo na ‘ya’yan wani fitaccen ɗan jihar Zamfara, Abubakar Bello Furfuri da suka sace. Harin da aka kai gidan tsohon Akanta Janar na jihar ya faru ne watanni huɗu da suka gabata.

A cikin faifan bidiyon da ke tafe, waɗanda suka yi garkuwa da su sun yi barazanar auren ‘yan matan ko kuma su tilasta musu su zama masu tayar da ƙayar baya. faifan bidiyon ya nuna ‘yan mata hudu a tsaye, ɗauke da makamai da harsashi.

KALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/BOweXpCsboc

Uku daga cikinsu sun sake da hijabi. Wadda ta iya Hausa cikinsu ta yi magana cikin kuka, an gano ta a cikin hoton da sukayi tare da ’yan uwanta da babanta. Yarinyar, wadda ɗaya daga cikin ‘yan fashin yaita katse ta tana magana, ta roƙi a ceci rayukansu, sannan ta bukaci hukumomi su ɗauki matakin da ya dace.

DAILY POST ta tattaro cewa ‘yan ta’addan sun ƙi sakin waɗanda aka kama duk da karɓar maƙudan kuɗaɗe daga iyalan. An yi garkuwa da mutanen ne a daren ranar 5 ga watan Yuni a unguwar Furfuri da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bungudu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kama mutane kusan 20; aƙalla rabin su mata ne. Maharan sun yi gaggawar ficewa daga ƙauyen kafin jami’an tsaro da aka tura yankin su isa wurin.

Leave a Reply