Hukumar NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da maganin tarin da ya ‘kashe’ yara a Gambia

1
576

Najeriya ta gargadi ‘yan kasarta da su guji yin amfani da wasu nau’ukan magungunan tari wadanda ake alaƙanta su da sanadin mutuwar mutane da dama a Gambia.

Ana zargin cewa magungunan iri huɗu, na kamfanin haɗa magani na Maiden Pharmaceuticals da ke Indiya, sun gurɓata ne da wasu abubuwa masu cutarwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargaɗi ƙasashen duniya kan su yi hattara da magungunan na yara.

Yanzu haka hukumar kula da ingancin abinci da mugunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta bukaci al’ummar kasar da su kaurace wa magungunan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NAFDAC ta ce duk wanda ya san ya yi amfani da wani daga cikin irin wadannan magunguna, kuma ya ji wasu alamomi da bai gane ba a tare da shi, to ya garzaya ya sanar da hukumomin lafiya.

Hukumar ta kara da cewa wasu daga cikin cututtukan da magungunan ke haifarwa sun haɗa da ciwon ciki, da amai, da gudawa, da gaza yin fitsari, da ciwon kai, da lalurar koda mai tsanani wadda ka iya sanadin mutuwa.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace ko akwai magungunan a kasuwannin Najeriya ba.

Magungunan tarin dai su ne na ‘Promethazine Oral Solution’, da ‘Kofexmalin Baby Cough Syrup’, da ‘Makoff Baby Cough Syrup’ da kuma ‘Magrip N Cold Syrup’.

A wata sanarwa da kamfanin magungunan ya fitar, ta ce ya yi takaicin matsalolin da magungunan suka haifar. Kamfanin ya ƙara da cewa ya bi duk wasu ƙa’idojin da aka gindaya na haɗa magani a ƙasar Indiya, kuma yana bayar da haɗin kai a binciken da ake gudanarwa.

Tuni dai Gambia ta fara janye magungunan daga kasuwanninta.

Ana alaƙanta magungunan tarin da yin sanadin mutuwar akalla yara 69.

Kuma hukumar lafiya ta nuna fargabar cewa ba a Gambia kawai ake amfani da magungunan ba.

1 COMMENT

Leave a Reply