Daga Fatima GIMBA Abuja
Kotun Shari’a ta Jihar Kano ta Bichi ta umurci rundunar ‘yan sandan Kano da ta ƙaddamar da bincike kan Mr 442, Safiyya Yusuf (Safara’u), Ado Gwanja da wasu mutane bakwai.
Neptune Prime ta samo rahoton cewa wannan yana ƙunshe ne a cikin takardar koke da kotu ta aika da umarni a watan 30 ga Agusta, 2022.
Sauran waɗanda suke cikin takardar koken sun haɗa da, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Murja Ibrahim, Ummi Shakira, Samha M Inuwa da Babiyana.
Lauyoyi 9 ne suka rubuta takardar koke inda suka roƙi kotun da ta ba da umarnin gudanar da bincike kan mawaƙan.
Idan dai za a iya tunawa dai a kwanakin baya Ado Gwanja ya fitar da wata sabuwar waka mai suna ‘Asosa’ wacce ta haifar da cece-kuce da tofin Allah tsine.
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci ‘yan sanda da su binciki mawaƙan Kannywood, Safara’u, Ado Gwanja, da sauransu […]
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci ‘yan sanda da su binciki mawaƙan Kannywood, Safara’u, Ado Gwanja, da sauransu […]