Hukumar ‘yan Sanda ta kama wadda ake zargin sace yara 15 a jihar Ribas

0
280

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama wata mata mai shekara 44 kan zargin satar yara 15 a kudancin Jihar Ribas ta ƙasar.

Ƴan sanda sun ce an sace yaran ne domin matar ta yi safarar su. Matar dai ta yi iƙirarin cewa tana da gidan marayu. Rahotanni sun ce yaran na tsakanin shekara huɗu ne zuwa 15.

Yan sandan kuma sun ce suna aiki tuƙuri domin tabbatar da cewa yaran sun koma wurin iyayensu.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Friday Eboka ya ce bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin yaran an sace su ne tun shekarun baya, ciki har da wani yaro mai shekara tara wanda aka sace daga kasuwa tun a 2020.

Leave a Reply