Daga Shafa’atu DAUDA, Kano
Hukumar Karota ta Jihar Kano tayi nasarar cafke wata tirela maƙare da barasa, a kan titin Bello Dandago dake kwaryar birnin Kano.
lJami’an karotan sun kama motar ne da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, a ƙoƙarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano.
Jami’an Hukumar ne suka sami nasarar cafke motar a lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗakko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya ɗakko.
Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.
Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Ɗan’agundi, ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci karo da su, wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba.
Ya ƙara da cewa za a ƙara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan, domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.
Ƙasa da mako guda hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maƙare da Giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (40) da kuɗinta ya haura naira miliyan arba’in 40.
Da zarar an kammala bincike za a miƙa Giyar ga Hukumar Hizba ta jihar kano domin ɗaukar mataki na gaba.