Matashi yayi sanadiyar yankewa budurwa ƙafa a Sokoto

1
820

Wani matashi me suna Aliyu Sunusi ya buge ɗaliba me suna Fatima Sulaiman, a yayin da yazo makarantar su taya abokansa, ‘yan ajinsu fatimar murnar gama jarabawar NECO, ta hanyar wasa da mota.

KU KALLI BIDIYON ANAN:https://youtu.be/SuTULzl4if4

Matashiyar mai shekara 20 daya takewa kafar dama da mota ranar da ta kammala rubuta jarabawar ƙarshe ta NECO a Sakkwato, ta ce ba za ta iya yafe masa ba.

Yanzu haka dai an yanke kafar, sai dai ta roki gwamnatin jihar da ta hukunta shi, kasancewar shi ba ma dan makarantar ba ne, zuwa ya yi wasa da mota da abokansa da suka kammala jarabawar.

Hoto: Nasiru Bello Sakkwato

Fatima Sulaiman

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here