Kotu ta bayar da belin babban akantan Najeriya da aka dakatar

0
263

Dafa Fatima GIMBA, Abuja

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin babban Akantan Najeriya da aka dakatar, Idris Ahmed tare da sauran wadanda hukumar EFCC ke tuhuma.

Da yake bayar da belin a yayin zaman shari’arsu a yau, alkalin kotun Justice Adeyemi Ajayi ya umarci mutanen da kada su bar yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma idan har suna son fita daga yankin na Abuja to lalle sai sun nemi izinin kotun ko kuma a soke belinsu.

Kotun ta kuma zartar da cewa dole ne su kiyaye da sharudan belin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriyar EFCC ta gindaya.

Idris da sauran wadanda ake tuhuma sun gurfana a gaban kotu a bisa zargin sata da almundahana har 14 da suka kai na kudi naira biliyan 109.5

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here