Shari’ar Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya

1
233

Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa bayan samun shi da laifin kisan dalibarsa, Hanifa Abubakar, mai shekara biyar a duniya.

A yau Alhamis, babbar kotun jihar Kano, a arewacin Najeriya ta yanke hukuncin bisa kisan da aka yi wa wata ƙaramar yarinya Hanifa Abubakar.

Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Dasambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.

Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.

Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A-Daidaita-Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi da ita.

An yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka ji ɗuriyarta.

A watan Janairu ne aka gano gawar yarinyar da aka sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

‘Yanda sanda sun tono gawarta tata wadda ake zargi Abdulmalik Tanko, mai makarantar  Noble Kids Academy, ya binne a wani rami.

An zarge shi da hada baki da Isyaku Hashim da matarsa Fatima Jibril da laifukan da suka hada da hada baki wajen aikata laifi, da satar mutum da kuma tsare yarinyar da suka sace ba tare da amincewarta ba da kuma kisan kai.

An kwashe kimanin watanni shida ana shari’ar wadda Mai Shari’a Usman Na’abba yake jagoranta.

Ta yaya aka gano Hanifa?

Tun lokacin da lamarin ya faru ne aka ƙaddamar da binciken hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na farin kaya na DSS da ƴan sanda da jami’an Civil Defence. Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda jihar Kano ya shaida wa manema labarai a ranar da aka gano gawar tata cewa jim kaɗan bayan sace Hanifa sai ɓarayin suka kira iyayenta suna neman kuɗin fansa har kimanin naira miliyan shida.

Bayan samun rahoton ne sai Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya haɗa taron gaggawa na manyan shugabannin tsaro don gano cewa an gano ƙarin dabarun tabbatar da tsaro a jihar Kano.

Daga nan kuma sai rundunar ƴan sanda ta tayar da tawagar ‘Kan Ka ce Kwabo’, wato Operation Puff Ader don tabbatar da kamo waɗanda suka sace yarinyar.

“Da aka ci gaba da bibiya aka yi ta aiki da har nasara ta kai aka kama mutum biyu da farko, wato Abdulmalik Muhammad Tanko mai shekara 30 da abokinsa Hashim Isiyaku mai shekara 37 da suke unguwar Tudun Murtala, kuma jami’an DSS suka yi nasarar kama su,” in ji DSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

“Daga binciken da aka fara ne Abdulmalik ya tabbatar da cewa Hanifa dalibarsa ce tana karatu a makarantar da yake koyarwa a Kwanar Dakata. Ya sace ta ne ya kai ta gidansa ya ɓoye ta har kimanin sati biyu, ya kuma nemi a ba shi kuɗi har naira miliyan shida.

“Ranar 18 ga watan 12 da ya fahimci ana so a gano cewa yarinyar tana tare da shi, don har gidansa ana ta bibiya an je, sai ya gaya mana (ƴan sanda) cewa ya ba ta guba ta sha ta mutu.

“Daga nan sai suka haɗa baki da wancan abokin nasa Hashim suka ɗauke ta suka sa a buhu suka kai ta wannan makarantar suka yi tono suka binne ta,” kamar yadda kakakin ƴan sanda ya ce.

DSP Kiyawa ya ƙara da cewa “sai a yau 20 ga watan Janairun 2021 ne muka yi nasarar kamo su.”

Kakakin ƴan sanda ya ce sun fara da yi wa Hashim tambayoyi ne inda ya tabbatar da cewa haƙiƙa Abdulmalik ya neme shi ya taya shi wani aiki cewa akwai abin da za su je su binne a buhu, kuma ya taimaka masa wajen yin tonon a cikin makarantar suka kuma binne.

Sannan ya gaya wa ƴan sanda cewa kafin ma wannan lokacin shi Abdulmalik din ya samu Hamshim shi da wata Fatima Jibrin Musa mai shekara 27 da ke zaune a Tudun Murtala, ya kuma ce musu su je su sato masa wannan yarinya, amma sun ce daga baya sun gaya masa ba za su yi ba.

1 COMMENT

Leave a Reply