Daga Fatima Abubakar MONJA, Abuja
Shi wannan salon sarrafa naman sunansa Suyan ruwa.
Abubuwan buƙata; Nama, tafarnuwa, albasa, masoro, citta, thyme, sinadarin dandano, da gishiri, a haɗasu a turmi a daka.
Da farko uwargida zata wanke nama, ta bar naman ya tsane da kyau kafin ta dauko kayan ƙamshin nan kika daka, sai ki zuba akan naman ki, ki juya shi sosai, ki bari yayi kamar minti talatin kafin ki sa a wuta, domin kayan qamshin da sinadaran dandano su ratsa naman.
Daga nan sai ki daura a wuta, zaki dinga motsa shi da muciya a haka zai nuna har ya fidda mai, sai a soya shi in mai bai fita dayawa ba zaki iya karawa.
Uwargida zata ci-gaba da juyawa har se ya soyu. Idan uwargida naso a ci a wannan lokaci, sai a tsame.
Sannan za a iya barinshi a cikin man shi, wato kitse, zai iya kaiwa shekara ba tare da ya lalace ba.
[…] KU KUMA KARANTA: Yadda Uwargida zata sarrafa naman sallah […]