Kotu ta yanke hukuncin kisa ga wasu ‘yan luwaɗi a Ningi

2
490

Wata babbar kotun shari’ar Musulunci dake Bauchi, arewacin Najeriya, ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan ta same su da laifin yi wa wasu yara faɗen luwadi a garin Ningi.

Kotun ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da mai sama da shekara 70, da wannan laifi, wanda suka amsa.

Sai dai wani jami’in kotun, ya ce babu wani lauya da ya wakilci mutanen a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.

Kwamandan Hisbah na karamar hukumar ta Ningi, Adamu Dan Kafi, ya bayyana cewa, an kama mutanen ne a kauyen Wada a watan Mayu, bayan da suka yaudari yaran da dabino da kuma kwakwa.

2 COMMENTS

Leave a Reply