Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
A WANI yunƙuri na karin samun zaman lafiya a bisa aikin jarida da bayar da sahihan rahotanni domin kawar da duk wata tarzoma, wata kungiya mai zaman kanta, Mercy Corps (MC) tare da haɗin gwiwar cibiyar sasantawa tsakanin addinai (IMC), reshen Jihar Kaduna sun horar da ‘yan Jaridu arba’in (40) kan yadda za a bayar rahoton rikice-rikice a Kaduna.
Taron horon wanda ya a cibiyar yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kaduna, ya kasance na yini biyu ne domin gina kwarin gwiwar ga yan Jaridu ta yadda za su rika bayar da rahoton yadda ake tada zaune tsaye ba tare da tada hankali ba.
A jawabinsa na maraba, Mista Godwin Okoko wanda ya wakilci darakta na kasa, MC Ndubisi Anyanwu ya bayyana cewa kungiyar wata kungiya ce ta duniya da ke kokarin samar da makoma mai kyau ta yadda kowa zai samu ci gaba.
Ya yi nuni da cewa, rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba ba za a iya misilta shi ba, don haka ake da bukatar ba da horon kara inganta karfin gwiwar ga yan Jaridun.
Ya bukaci mahalarta taron da su mai da hankali kan horarwa da aiwatar da ilimin da suka koya a cikin rahotanninsu.
Tun da farko a nata jawabin, shugabar cibiyar kungiyar ‘yan Jaridun (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Halilu, ta bayyana cewa sana’ar aikin jarida na bukatar a rika ba da horo akai-akai domin inganta kwarewar kwararrun ‘yan Jaridu don gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ta ce, “batun horon na ranar ya dace, duba da yadda a ‘yan kwanakin nan aka kama wasu ‘yan jarida ko kuma daure su a yayin gudanar da ayyukansu.
“Da yawa daga cikinsu sun kasance wadanda abin ya shafa saboda rashin sanin ya kamata a kan rahoton la’akari da rikice-rikice.
“Kyakkyawan aikin jarida na bukatar mu gudanar da tantancewa yayin da ake fama da rikici don fahimtar bangarorin da abin ya shafa da kuma rawar da suke takawa a lamarin kafin mu watsa wani bayani,” in ji ta.
Hajiya Halilu ta kara da cewa kafafen yada labarai su ne matakin iko na hudu a duniya kuma madubin al’umma inda ta bukaci kwararrun da su rika bin ka’idojin sana’ar yayin da suke bayar da rahotannin rikici.
Hakazalika, Malam Jamilu Yahaya Jega, Daraktan Shiyya na Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC) ya bayyana cewa akwai dokoki da tsare-tsare da ke tafiyar da rahoton rikice-rikice.
Yahaya wanda ya yi magana kan tsari da manufofi na hukumar don magance rahotannin rikice-rikice, ya bayyana cewa ana sa ran manema labarai su gabatar da labarai da sharhi kan rikici ko gaggawa cikin kwarewa.
Ya ce “dangane da wannan makala da aka gudanar, ina saran duk wanda yazo wannan taro ya karu don ba mu su har ni kaina na karu saboda akwai jami’ai da dama sun yi bayanai wanda akasarin mutanen da ba su da kwarewa sun karu kuma an gudanar da shi ne don inganta aikin Jarida.
“Kuma abin da na yi magana a kai shi ne a kiyaye tsabtace harshe amma mutane da dama su kan yi kuskure, musamman ma Kafafen yada labarai na wannan zamani domin zamani ne wanda yake tattare da kaulubale, amma mutane da dama su kan yi ko oho da wannan kalubalen sai fadi abinda aka gardama a wannan zamani.”
“To Dokoki suna nan, wanda ya kamata a kiyaye harshen su domin a tsabtace irin kalaman da ale yadawa saboda bai halattaba ga dan Jarida ya bada damar a ci zarafin wani, bai kamata ba a furta kalamai batanci ga wani, bai kamata ba a fadi kalma wacce za ta tunzura Jama’a, bai halattaba ga dan Jarida ya bada dama a riki amfani da kafar yada labarai domin isar da sako wacce za ta kawo rudani a cikin Jama’a.
Mahalarta taron sun nuna jin dadinsu ga kungiyoyin biyu da kuma kungiyar NUJ da suka shirya horon inda suka ce ya dace kuma ya kamaci a ci gaba da gudanar da irin wannan horaswan izuwa lokaci zuwa lokaci.
[…] KU KUMA KARANTA: An Gudanar Da Taron Horas Da Yan Jaridun Kaduna Kan Yanayin Yada Labaran Rikice-Rikice […]