Gwamna Zulum Ya Gabatar Da Sunayen Kwamishinoni 20 Ga Majalisar Dokokin Jihar Don Tantance Su

0
398

Daga; Sani Gazas Chinade, Maiduguri.

GWAMNA Babagana Zulum na Jihar Borno ya mika sunayen kwamishinoni Ashiru (20) ga majalisar dokokin jihar (BOSHA) domin amincewar ta da nufin tantance Su.

Majalisar zartaswa ta Jiha mai mambobi 20 ta ruguje ne a watan da ya gabata a yayin gudanar da zabukan share fage ta 2023 na jam’iyyar APC na Jihohi da aka gudanar kwanan nan.

Da ake gabatar da sunayen a Majalisar, kwamishinonin nadin, a ranar Talata a harabar majalisar da ke Maiduguri, Wakilinmu ya lura cewa “Yawancin tsoffin kwamishinoni da suka halarta suna cikin wadanda Majalisar ta tantance kuma ta amince da su a cikin shekaru uku da suka gabata”

Jerin sunayen kwamishinonin da aka mika sun hada da sabbin mutane uku da aka nada a Majalisar wadanda suka hada da Farfesa Mohammed Arabi, wanda shi ne babban daraktan kula da asibitocin jihar Borno da Pogu Lawan Chibok da kuma Dakta Ali Bunu Mustapha.

Domin tabbatar da ci gaba da gudanar da mulki tare da karfafa ribar dimokuradiyya, an saka tsoffin kwamishinoni 17 a cikin wadanda aka gabatar domin amincewa da su wanda suka hada da Mustapha Gubio, Adamu Lawan, Yerima Saleh, Lawan Wakilbe, Kaka Shehu Lawan da Sugum Mele.

Wadannan kwamishinonin da aka nada sun yi aiki a ma’aikatun sake ginawa, gyarawa da sake tsugunarwa (RRR), kudi, muhalli, ilimi, shari’a da kananan hukumomi da masarautu.

Sauran wadanda aka zaba cikin tsofaffin kwamishinoni don amincewa sun hada da Zuwaira Gambo wacce ta kasance tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata, Tijjani Goni, Sufuri, Babagana Malumbe, Kimiyya da Fasaha, Yerima Kareto, Kasuwanci da yawon bude ido, Saina Buba na Matasa da Wasanni, Yuguda Saleh of Ma’aikatar Gidaje da Babakura Abba Jato na Labarai.

Da yake jawabi ga manema labarai, Kakakin Majalisar, Rt Hon Abdulkarim Lawan ya ce, “Bisa tanadin sashe na 192 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999, majalisar ta karbi bukatar majalisar zartaswa da domin tabbatar da sabuwar majalisar wanda aka nada kwamishinoni.

“Tare da kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangaren Zartarwa, ‘Yan Majalisu da na Shari’a, ina so in tabbatar wa mutanen Jihar Borno cewa Majalisar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tantance wadanda aka nada tun daga mako mai zuwa ( Talata 21 ga watan Yuni 2022) domin tabbatar da doka da oda.

Leave a Reply