An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Cibiyar Kungiyar NUJ-NNN Ta Kaduna

0
474

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SHUGABAN Kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kaduna, Hajiya Asma’u Yawo Halilu, ta rantsar da sabbin Shugabannin Cibiyar Kungiyar Yan Jaridu ta kamfanin Jaridar New Nigeria Newspapers NNN da Gaskiya TaFi Kwabo dake Kaduna.

An gudanar da taron bikin Kaddamar da sabbin Shugabannin ne a harabar kamfanin Jaridar ta NNN-GTK a ranar laraba, biyo bayan gudanar da zaben cike gurbin Kujerar Shugaban Kungiyar da Sakataren da aka yi bayan tsofaffin shugabannin Kungiyar sun yi murabus sakamakon samun gurbin wani matsayi a Uwar Kungiyar ta NUJ da su ka yi.

Da take jawabi a wajen taron, Shugabar kungiyar ta NUJ Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo, ta bayyana cewa ya zame mata dole ne ta halarci wannan taron kasancewar ta mace ta farko a matsayin shugabar Kungiyar, kana iya ma Shugaban cibiyar Kungiyar ta NNN ta kasance mace ce yar uwarta kuma ita ma ta farko a wannan cibiyar Kungiyar.

Ta kara Jaddada Jan hankalin sabbin zababbun Shugabannin Cibiyar Kungiyar da su yi biyayya ga uwar Kungiyar da kuma gudanar da ayyukansu a matsayin Kwararru kamar yadda wannan sana’ar ta aikin Jarida ta tanada.

Sabbin Shugabannin da aka zaba a zaben cika gurbin Cibiyar Kungiyar sune Kwamared Funmi Aderinto, a matsayin sabuwar shugabar Kungiyar da Kwamared Usman Nasidi a matsayin sabon Sakataren Cibiyar Kungiyar ta NUJ-NNN Kaduna.

Ta ce “a matsayina na mace ta farko wacce ta fara shugabantar Cibiyar Kungiyar masu dauko rahotanni a Kaduna na wani dan lokaci, kana a yanzu na sake zaman Shugaban Kungiyar ta NUJ reshen Jihar Kaduna, yasa na ga ya dace na zo bikin rantsar da shugabar wacce ta ke mace ta farko ta cibiyar Kungiyar NNN.”

Asma’u, ta shawarci ‘ya’yan Kungiyar da ma’aikatan kamfanin gidan Jaridar da su kasance masu marawa sabbin Shugabannin goyon baya tare da basu duk irin hadin kan da ya dace domin tafiyar da al’amuran kungiyar ta hanyar da ta dace.

A nasa bangaren, Amos Matthew tsohon Shugaban kungiyar NNN chapel, ya yi kira ga shugabar Kungiyar ta Kaduna, da ta taimaka wa kamfanin gidan Jaridar ta NNN-GTK a gwagwarmayar da suke yi a halin yanzu da ofishinta, ya kuma shawarci sabbin zababbun da su yi aiki tare da hadin gwiwar Kungiyar.

Babban shugaban ma’aikata na yan Jaridun kamfanin, Malam Zubairu Sada da ya ke jawabin maraba da shugaban kungiyar Yan Jaridu na Jihar, ya taya ta murnar nasarar da ta samu, ya kuma bada tabbacin kamfanin da cibiyar Kungiyar na son taimakawa kungiyar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply