Muhalli: Wani Dan Najeriya Na Shuka Nau’in Bishiyoyi Sama Da Dubu 100.000 A Duk Shekara

0
360

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WANI hamshakin attajiri dake Jihar Kaduna a Kasar Najeriya, Al-amin Shehu, kuma ya ke da matakin karatun digiri, ya yi watsi da aikin farar fata, yayin da ya rungumi yin shuka da sayar da itatuwan domin dogaro da kansa, tare da tallafa wa gwamnati, kungiyoyin farar hula na Najeriya, kungiyoyi masu zaman kansu domin yaki da sauyin yanayi, bala’in ambaliya, kwararowar hamada, wanda aikin sare dazuka da lalata muhalli ke shafar rayuwar Bil-Adama da sauran kungiyoyin agaji.

A cewarsa a kowace shekara, sama da nau’ikan tsire-tsire daban-daban dubu dari yake shukawa tare da sayar wa dubban mutane da nufin dasa su a gida, tituna, da sabbin wurare domin ceton dan Adam daga dumamar yanayi da sauran kalubalen muhalli.

Al-amin, wanda bayan ya kammala karatunsa, ya rungumi sana’ar shuka iri da sayar da bishiyu domin ya kare kansa kuma ta wannan sana’a yake samun abin da yake samu na rayuwa kana a cikin kowane wata 6, yana samar da nau’ikan itatuwa dubu hamsin.

Ya kara da cewa ba ya son duk wani aikin gwamnati domin yana jin dadin abin da yake samu a kasuwanci, kuma hakan ya sanya ya ke kalubalantar wadanda suka kammala karatun digiri dinsu da zama masu kirkire-kirkire ta yadda zasu iya dogaro da kansu.

Bugu da kari, ya yi da kira ga gwamnati da ta samar da yanayin da zai sa wadanda suka kammala digiri su kasance masu dogaro da kai.

Hakazalika, wani masanin kimiyyar climatologist, darektan masu ba da rahoto kan yanayin yanayi na Afirka, Kwamared Nurudden Bello, ya buƙaci yan Najeriya da su dasa itatuwa da yawa a bana, domin yaki da kwararowar hamada, da rage dumamar yanayi.

Ya yi nuni da cewa dazuzzuka da dama a Arewacin Najeriya sun koma saharar hamada sakamakon rashin hankali da mutane suke yi na sare itatuwa.

Yayin da yake jaddada bukatar ‘yan Najeriya su rungumi dabi’ar dashen itatuwa a cikin al’ummarsu, ta yadda za a ceto muhalli daga bala’in ambaliyar ruwa, zaizayar kasa, da sauran kalubalen da suka shafi muhallin da ke cikin ruwa, ya nuna rashin jin dadinsa kan karuwar bukatar sana’ar sayar da itace da gawayi a kasar nan.

A karshe, ya yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su rungumi amfani da makamashin zamani da sauran hanyoyin amfani da murhun girki.

Leave a Reply