Dawakin Tofa, Tofa Da Rimin Gado, Canji Yazo

0
321

Daga; Jabiru Hassan, Dungurawa.

BABU shakka, kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da Kuma Tofa sun kasance mazaba ta tarayya wadda Kuma ta sami wakilai da suka gudanar da wakilci gwargwadon iyawar su, tun lokacin da Najeriya ta koma Kan hanyar dimokuradiyya a shekara ta 1999.

Haka Kuma mutanen wannan mazaba sun kasance masu matukar son zaman lafiya da kwanciyar hankali da Kuma bin dokokin kasa wanda hakan ta sanya a tarihi irin na siyasar wannan zamani ba a taba samun wani rikici kan wani shugaba ba duk da yadda ake samun mabanbantan ra’ayoyi.

A wannan tsokaci da na fara, zan bayyana yadda wannan mazaba mai kananan hukumomi guda uku masu Albarka watau Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa suke da ra’ayin samun chanjin wakilci a majalisar tarayya a zabukan shekara ta 2023 idan Ubangiji ya nuna mana.

Duk da cewa wakilan da suka wakilci wannan mazaba sun yi kokari sosai wajen kawo abubuwa na ci gaban yankin, sai dai mafiya yawan mutanen dake mazabar sun bayyana cewa yana dakyau su Sami chanji na dan majalisar wakilai domin shi ma ya jarraba nasa kokarin duba da cewa kowane dan kasa yana da damar ya tsaya takara ko Kuma ya zabi shugabanni.

Dimokuradiyya ta bada dama kowa ya nemi madafar iko domin watakila yana da wata gudummawa da zai iya bayarwa wajen ciyar da kasa gaba musamman magana ta aikin majalisa wanda kowa yasan cewa aiyukan yan majalisa shi ne yin dokoki da tabbatar da ganin wadannan dokoki sun sami kulawa bangaren zartaswa domin kyautata zamantakewar al’umma.

Sannan dan majalisa yana da iko ya gabatar da wasu bukatun al’ummar sa a matsayin sa na wakilin su a majalisa walau ta jiha ko tarayya domin mafiya yawan abubuwan da yan majalisa ke yi shi ne ke bayyana kwazon kowane wakili bayan gabatar da wani kuduri a zauren majalisar domin neman amincewar abokan aiki watau sauran wakilai da aka tura daga sassa daban-daban na kasa.

Yana dakyau idan dan majalisa ya gudanar da wakilci Karo biyu zuwa uku, to al’umma su yi kokarin nemo wani ya canje shi saboda shi ma yaje ya bada tasa gudummawar wajen wakiltar mutanen sa domin Ina ganin ta haka ne za a ci gaba da tafiya kan doron dimokuradiyya kamar yadda abin yake a sauran kasashen da suka ci gaba ta fuskar siyasa.

Nayi yunkuri na fara wannan bayanai ne saboda yadda naji cewa al’ummar kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa sun nuna bukatar samun canjin wakilci musamman na mutumin da zai wakilci mazabar a majalisar wakilai ta tarayya a shekara ta 2023, tare da nuna godiya ta musamman ga wakilin dake kan wannan kujera watau Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe saboda kokarin da ya yi tun daga shekara ta 2007 zuwa yau dinnan.

Bugu da kari, yanzu haka matasan wadannan kananan hukumomi na Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa sun kafa wata kungiya mai suna ” DTR Chanji Yazo” domin goyawa mutumin da zai tsaya takarar wannan kujera baya irin na siyasa domin shi ma ya bada tasa gudummawar a matsayin sa na dan kasa wanda kuma yake da damar ya yi zabe ko a zabe shi.

Kafin in kammala wannan tsokaci, zan yi amfani da wannan dama domin kara bayyana cewa canji a siyasa alheri ne, sannan a wasu lokutan, idan an sami canji, kwalliya tana kara biyan kudin sabulu musamman ganin cewa lokaci ya yi da al’ummar mazabar Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa zasu canza wakilin su na majalisar wakilai domin a bashi damar shakatawa wani kuma ya dora daga inda zai ajiye.

A karshe, kamar yadda kungiyar “DTR Chanji Yazo” ta fara aiyukan ta, nan gaba kadan kuma zata fara zagaya kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa domin bayyana manufofin ta na marawa mutumin da zai yi takarar kujerar baya domin wakilcin mazabar duba da yadda zabukan 2023 suke Kara matsowa kusa.

Jabiru Hassan Dungurawa, Karamar Hukumar Dawakin Tofa. medialink57@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here