Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.
AN bayyana Gwamnan Jihar Zamfara a matsayin jagora kuma mujaddadin tabbatar da ci gaban kawo alkairi a Jihar da kasa baki daya.
Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara Shawara a kan harkokin hulda da yarjejeniya da kasashen waje, Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wata tawagar manema labarai a Kaduna.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya ci gaba da cewa hakika Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawalle ya yi rawar ga ni da za a iya bayar da labari ga duniya irin kokarin da ya aiwatar wajen ci gaban Jihar.
Ya ce, “hakika kashin bayan ci gaba da zaman lafiya shi ne a samu sulhu da za a iya yin tafiya tare kai a hade tsakanin jiga- Jigan Jihar Zamfara.
Gwamna Matawalle hakika ya ajiye tarihi gagarumi domin a tarihin Jihar Zamfara ba wani wanda ya jawo mutanen da suka fandare amma ya jawo su a ta fi tare domin Jihar Zamfara da kuma al’ummarta baki daya su samu ci gaba kamar shi.”
“Ya jawo tsofaffin Gwamnoni irinsu Ahmad Sani Yariman Bakura, Mahmuda Aliyu Shinkafi, Abdul’Aziz Yari Abubakar da kuma su Sanata Marafa da sauransu da dama duk domin a ciyar da Jiha gaba wannan babban tarihi ne da kowa ke alfahari da shi sosai.”
Dokta Suleiman Shinkafi da ke ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan hulda da yin yarjejeniya da kasashen waje, ya ce a yanzu dai Allah ya amince kowa daga cikin wadannan Jiga- Jigan sun hango ci gaban Jihar Zamfara kuma sun dunkule wuri daya wannan abin alfahari da farin ciki ne matuka.
Dokta Suleiman Shinkafi ya kara da cewa babban dalilin da suka hango ya sa wadannan jiga – Jigan mutane a Jihar Zamfara suka dunkule wuri guda shi ne domin kawai Jihar ta samu ci gaban da ya dace ta samu ne.
“Saboda idan sun zauna a yanayi na baraka ba za a samu ci gaban Jihar Zamfara ba amma a halin yanzu sun dunkule wuri guda kuma jama’a na farin ciki da wannan haduwa ta su domin Talakawa za su samu sauki kwarai”, Inji Dokta Shinkafi.
Ya ce muna nan tare da su mun rungume su za kuma mu ta fi tare har a cimma duk wata nasara a Jihar Zamfara.
Game da masu cewa wai ko jam’iyyar APC ta hango faduwa ne a Jihar Zamfara ya sa suka ba da kai? Sai Dokta Shinkafi ya ce ” kamar dai yadda kowa ya sani ne jam’iyyar APC ba za ta fadi ba a Jihar Zamfara, kasancewar babu wata jam’iyya mai tasiri a Jihar Zamfara da ta wuce APC, ba kuma wani Gwamna mai tasiri a Jihar Zamfara da ya kai Gwamna Matawalle saboda haka maganar faduwa ma ai ba ta taso ba mun dai dubi cewa Allah ne ke yin yadda yaso a lokacin da yaso saboda haka dukkan mu baki daya kasa za mu ta fi bayan mutuwa kowa ya girbi abin da ya shuka.
“A kan haka ne Gwamna Matawalle kancewarsa mutum mai tsoron Allah, lissafi da nazari ya ga cewa mulki na duniya fa ba wani abu ba ne shi ya sa ya ga dacewar a zauna tare da sauran yan uwa ayi tafiya tare domin a ceci talakawan Jihar Zamfara kowa ya samu ci gaba saboda duk fadan da ake yi Talakawa ne ke shan wahala”. Inji shi.
Game da batun girin – girin kuwa sai ya fayyace cewa ” su a nasu matsayin ba girin- girin ba, ta yi mai su a nasu wuri har ruwa ma ta kara domin daman can tuni aka rarraba mukamai, mai girma tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari zai ta fi Sanata kuma tsohon Sanata Kabiru Marafa shi ma zai ta fi Sanata an kuma ba wadanda suke nema da dai wani abu mai kama da hakan an ba su hakuri kuma sun hakura an ba su yan majalisu na tarayya da yan majalisu na Jiha kadan domin shi Gwamna ya dace ya rike yan majalisu na Jiha duk baki daya domin shi zai yi aiki da su.
Don haka ya dace ya rike wadanda ya Sani, saboda haka mu tarigaya ta yi mai har ta batse kuma ina tabbatarwa da jama’a an zauna lafiya domin an raba mukamai tun da dadewa kuma da izinin Allah, haka za a ta fi nan da dan lokaci kadan talakan Zamfara zai ga abin mamaki kwarai”.
Saboda haka duk wanda ka ga ya ce baya son wannan hadewar da aka yi baya son zaman lafiya don akwai wanda ya ce bai amince ba misali dan majalisar tarayya mai wakiltar Shinkafi da Zurmi Bello Hassan ai bai amince da hakan ba domin ya ga cewa zaman sulhun da aka yi bai yi masa ba sai ya koma PDP, kuma komawarsa PDP ba za ta hana mu kayar da shi ba”,.