Maniyyatan Aikin Umrah Sun Zargi Azman Air Da Zubar Da Su A Kano

1
424

Daga; Rabo Haladu.

WASU maniyyata aikin Umrah sun zargi kamfanin sufurin jiragen sama na Azman Air da zubar da su a Kano, suna watangaririya bayan ya gaza kai su ƙasa mai tsarki.

Maniyyatan, waɗanda suka ce sun kai ɗaruruwa, sun koka kan rashin ba su ko da makwanci bayan sun baro gidajensu daga Jihohi daban-daban.

Wasu maniyyatan sun shaida cewa sun shiga mawuyacin hali bayan Azman Air ta zubar da su a Kano ba tare da yi musu bayani a kan tsaikon da aka samu na jigilarsu zuwa kasa mai tsarki ba.

Daya daga cikin fasinjojin, ya shaida cewa, kusan kwanansu biyu jibge a Kano, kuma akwai wadanda daga cikinsu suka je Kanon daga Jihohi kamar Sokoto da Kebbi da Zamfara da Borno har ma Abuja, babban birnin tarayya.

Yace “Da muka je Kano cikin dare mun zauna filin jirgin saman Kano har zuwa 11:30 na dare, ba wanda ya ce mana uffan, haka muka yi ta zaman jira har muka gaji, daga nan ne muka shiga gari muka nemo otel don mu kwanta.”

Fasinjan ya ce sun je ofishin Azman Air da ke Zaria Road sun tarar an kulle, haka suka kasance babu wanda ya ce musu komai har sun gaji da biyan kudin otel.

Sai dai mataimakin babban manajan kamfanin na Azman Air, Nuradden Aliyu, ya shaida cewa jinkirin da aka samu ya samu asali ne sanadin fashewar tayar jirginsu a makon da ya wuce a kasa mai tsarki lamarin da ya haddasa tashin wuta amma an yi nasarar kashe ta.

Yace wannan hatsari ne ya shafi lafiyar jirginsu na jigilar aikin Umrah ko da yake tuni aka kammala gyaransa a ranar Litinin 18 ga watan Afrilun, 2022.

Mataimakin babban manajan kamfanin na Azman Air, ya ce ana sa ran tasowar jirgin zuwa Najeriya don ci gaba da aikin jigilar a ranar Talata 19 ga watan Afrilun, 2022.

Ya ce sai da suka tuntubi wasu kamfanonin jiragen amma saboda yanayin da ake ciki na jigilar zuwa Umrah, ba su samu jirgin da zai taimaka musu ba, shi ya sa suka tsaya tsayin daka wajen ganin an gyara na su.

Nuradden Aliyu ya ce,” Duk wani matsayi da muke ciki mu kan sanar da fasinjoji cewa mun daga jirginsu kada suje filin jirgin sama.”

Ya ce an samu rashin fahimta tsakaninsu da maniyyatan, saboda shi aikin Umrah, kamfanonin da ke shirya tafiye-tafiye ne ke sayen tikitin tafiya, su kuma a nasu bangaren sun sanar da duk wadanda suka kamata.

Fasinjojin da aka ta tattaunawa da su, sun bukaci kamfanin Azman Air da ya biya su kudaden da suka kashe kamar na wajen kwana da suka kama a Kano tare da sauran wahalhalun da ya janyo musu.

To amma kamfanin ya ce ba bu wani hakkin fasinja da zai salwanta a hannunsa.

1 COMMENT

Leave a Reply