Sardaunan Badarawa Ya Raba Shinkafa Da Kudi Na Kusan Kimanin Naira Miliyan 45

0
431

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

TSOHON Shugaban riko na Kaduna ta Arewa, Honarabul Usman Ibrahim wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa, ya raba buhuhunan shinkafa da kudi na kusan kimanin Naira Miliyan 45 ga wakilai na Jam’iyyar PDP a shiyyar Kaduna ta tsakiya.

Honarabul Ibrahim wanda shi ma dan takarar Sanata ne na shiyyar Kaduna ta tsakiya ya kuma bayar da wasu sabbin motoci uku a lokacin da yake bayyana ra’ayinsa na tsayawa takara a Kaduna.

Yayin da yake ba da tabbacin sanya muradin masu goyon bayan Jam’iyyar a gaba, dan takarar Sanatan ya bayyana cewa, idan wakilan suka zabe shi ya lashe Zaben fidda gwani, jam’iyyar PDP za ta samu gagarumin rinjaye wajen lashe Zaben gama gari domin a cewarsa farin jini da kwarjinin da ya bayyana cewa ya na da shi zai kasance wani abun da zai iya zama dalilin da zai sa a zabe shi don haka dole ne a yi la’akari da ‘yan takarar da ke neman mukaman Zaben.

Ya yi nuni da cewa tuni jam’iyyar adawa a jihar ta fara shirin korar jam’iyyar APC daga gidan gwamnatin Kaduna da duk wasu mukamai da za su yi takara.

Dan siyasar ya kara da cewa PDP za ta ci gaba da zama a gidansa, inda ya tuna yadda ya rasa gidansa dauke da motoci goma biyo bayan rikicin zaben 2011 a Kaduna da sauran Jihohin Arewa.

Sardaunan Badarawa wanda kuma ke rike da sarautar San-turakiin Hausa na gargajiya, ya lura cewa siyasa ta shafi yi wa jama’a hidima ne a matakin kasa wanda ya ce bukatunsu ya kamata su zama abin damuwa ga aikin duk wani zababben shugaba.

Mai ba da agajin ya ce ƙara darajar rayuwar jama’a shi ne ya mayar da hankali a kai bisa harkokin jama’a.

Acewarsa, ya kasance mai goyon bayan PDP tun bayan komawarsa jam’iyyar da ya bayyana a matsayin Jam’iyya mai Karfi wacce za ta yi nasara wanda hakan yasa yake son jam’iyyar adawa mai karfi da za ta iya kwace mulki daga hannun APC.

Hon. Ibrahim ya yi alkawarin cewa ba zai ba yankin Kaduna ta tsakiya kunya ba idan har aka ba shi wakilcin shiyyar Sanata a zaben 2023.

Wani daya daga cikin wakilen wanda ya bayyana kansa a matsayin Musa Lawal ya yabawa dan siyasar bisa karamcinsa da jajircewarsa ga jam’iyyar, inda ya sha alwashin tara sauran wakilai domin samun nasarar Sardaunan Badarawa a zaben fidda gwani da na kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here