JABIRU A HASSAN, Daga Dutse.
AN kaddamar da shirin allurar rigakafin dabbobi na bana a karamar hukumar Buji inda aka kiyasta cewa dabbobi dubu 60 ne za a yiwa rigakafin a fadin karamar hukumar.
A jawabinsa wajen kaddamar da allurar rigakafin, shugaban karamar hukumar ta Buji Alhaji Abdullahi Suleiman Yayari, ya sanar da cewa karamar hukumar za ta ci gaba da gudanar da allurar dabbobin domin tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya kamar yadda manufofin shirin suke.
Sannan ya yabawa makiyayan dabbobin da mutanen yankin saboda yadda suke kai dabbobin su wajen allurar wanda a cewar sa, hakan yana taimakawa a sami ribar kiwo musamman a wannan lokaci da ake ciki na bukatar dogaro dakai.
Abdullahi Yayari, ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Jigawa bisa kokarin da gwamnatin sa ke yi wajen inganta hanyoyin dogaro dakai wanda a hakane tattalin arzikin al’umma yake bunkasa.
A nasa tsokacin, shugaban sashen gona da albarkatun kasa na karamar hukumar, Malamud Hassan Jibrin Garkuwa Kafin Hausa, ya sanar da cewa an raba karamar hukumar kashi uku domin samun nasarar zagaye kowane lungu domin yin wannan rigakafi watau shiiyar Gantsa da Buji da kuma Yayari, tare da tabbatar da cewa an tanadi dukkanin kayan aikin da ake bukata kan wannan rigakafi.
Mahamud Hassan Garkuwa ya yi jinjina ga shugaban karamar hukumar ta Buji da mataimakan sa bisa yadda suke kokari wajen bunkasa yankin ta kowane fanni, kana ya nuna gamsuwar sa bisa yadda mutanen yankin suke baiwa shirin rigakafi goyon baya.
Shima da yake sanya albarka kan shirin rigakafin, Hakimin Buji Alhaji Nuhu Sarki Lamido godiya ya yi ga majalisar karamar hukumar saboda kokarin da take yi wajen bunkasa sana’ar kiwo da kuma inganta rayuwar al’umma ba tare da nuna kamala ba.
Wasu makiyaya da suka zanta da manema labarai watau malam Saleh Wada Yaroji da Haruna Kukuma sun bayyana karamar hukumar Buji a matsayin uwa a garesu saboda taimaka masu da take yi wajen bunkasa sana’ar su ta kiwo da kula da dabbobin su.