Harin Jirgin kasa: NAWOJ, Ta Yi Allah-Wadai Da Kakkausar Muryar Bisa Mummunar Ta’addancin

2
384

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR mata yan Jaridu ta Najeriya (NAWOJ) reshen Jihar Kaduna, ta bayyana matukar damuwarta game da harin da wasu yan Bindiga suka kai wa Jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna wanda ke dauke mutane fasinjojin da ba su ji ba ba su gani ba a daren Litinin, 28 ga Maris, 2022.

A wani sakon da aka rabawa manema labarai a garin Kaduna dake dauke da sa hannun Shugabar Kungiyar, Fatima Aliyu, da Sakatariyar Maureen Sheyin, sun jajantawa iyalan fasinjojin da suka rasu, da wadanda suka jikkata da wadanda aka yi garkuwa da su a wannan lamari mai cike da ban tausayi.

Kungiyar ta (NAWOJ) na fatan za a nemo wadanda harin ta’addanci ya shafa wanda har ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin Naira a fadin Jihar Kaduna.

Ta ce “A matsayinmu na ’yan uwa mata kuma mata masu sana’ar aikin Jarida da kishin al’umma masu son zaman lafiya da ci gaba, muna yin Allah wadai da kakkausar murya bisa irin wannan aika-aikar na dabbanci ga ‘yan kasa masu zaman lafiya da bin doka da oda wanda a fili ake yi domin haifar da dawwamammen tsoro a zukatan ‘yan Najeriya masu son zaman lafiya.

A daidai lokacin da kungiyar ta amince da cewa kasar nan, musamman Jihar Kaduna ta shiga cikin mawuyacin hali, kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su dage da jajircewa da mayar da hankali wajen tunkarar wadannan matsaloli masu ban takaici da kuma ci gaba da yin domin Allah shiga tsakanin nagari da mugu.

Kungiyar ta yi kira ga ‘yan Jihar da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro tare da ba su bayanai masu amfani da sahihanci game da mutanen da ake zargi ko ba a gane motsinsu ba don mayar da martani cikin gaggawa.

Kungiyar ta yabawa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna bisa kokarin da suke yi na tunkarar kalubalen tsaro, kana ta bukace su da su kara kaimi wajen magance wadannan kalubale. Har ila yau, ta umurci gwamnatocin biyu da su tunkari masu zagon kasa ga tsaron kasarmu.

Acewar Shugabar Fatima, hukumomin Jami’an Tsaron sun cancanci a yaba musu kan yadda suke yin taka-tsantsan wajen fuskantar barazanar tsaro a gidajen kallo daban-daban na kasar nan, kana ta bukace su da su ci gaba da juriya.

A karshe, Kungiyar NAWOJ ta yi addu’ar fatan Allah Ya jikan wadanda suka mutu sakamakon hare-haren ‘yan ta’addan, kana da samun sauki ga wadanda suka jikkata, da fatan Allah Ya kubutar da wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane, su dawo cikin koshin lafiya.

2 COMMENTS

Leave a Reply