Rundunar Soji Ta Karyata Zancen Sojin Da Ya Wallafa Faifan Bidiyo A Yanar Gizo

0
422

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

RUNDUNAR sojojin Najeriya (NA) ta bayyana cewa an jawo hankalin ta kan wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda wani soja a ranar Laraba, 30 ga Maris, 2022 ya yi ikirarin cewa abokan aikinsa sun yi watsi da shi yayin gudanar da ayyuka sabanin ikirari da tunanin da sojan ya yi a cikin faifan bidiyon.

A wani sakon da rundunar ta wallafa a shafinta na sada zumunta da ke dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji Birgediya Janar, Onyema Nwachukwu, ta bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa faifan bidiyon wani shiri ne na kare kansa daga zargin zama matsoci, inda ya yi watsi da abokan aikinsa a wani samame da ake yi a garin Gurara na jihar Neja.

Idan dai za a iya tunawa, a baya-bayan nan ne dakarun hukumar ta NA, suka gudanar da aikin share fage a karamar hukumar Gurara ta jihar Neja. Ta ce abin takaicin shi ne yayin gumurzun sojan ya yi watsi da abokan aikinsa tare da tserewa a fili na nuna tsoro da yiwuwar zagon kasa, wanda ya saba wa ka’idojin aikin soja.

Da yake jin girman abin da ya yi da kuma sakamakonsa, sojan ya boye a sirranci ya yi bidiyon ya saka a yanar gizo da zummar kokarin jawo hankalin jama’a bisa karya tare da boye laifin abin da ya aikata na tsoro.

Matakin sojan ya yi daidai da cin amanar aikin rundunar da abokan aikinsa wanda suka yi daidai da rukunin aikin soji, musamman a lokacin aiki. Don haka halin sojan ya sabawa ka’ida da kimar aikin soja.

Rundunar ta nuna alhinin damuwar rashin sanin dalilin yin faifan bidiyon a wannan halin, da kuma manufar yin kuskuren abin da ya faru tsakanin sojan da abokan aikinsa.

Acewar sakon, Sojan ya koma rundunarsa kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano dalilan da suka sa ya aikata rashin da’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here