Rashin Wadatattun Kayan Aiki Da Taimako Ne Cikas A Aikin Katin Zaben Rigasa – Kungiyar RAAF

0
385

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA kungiyar Azama da wayar da kan al’umma (RAAF) dake Gundumar Rigasa Kaduna, ta koka bisa rashin samun wadatattun kayan aiki da mutane masu taimakawa wajen gudanar ayyukan yin katin Zabe ne ke zame musu cikas yayin cimma burinsu na samun nasarar aikin.

Kungiyar (RAAF) ta yi wannan korafin ne a ranar lahadi, yayin da take zaman taron ta na mako-mako da ta saba gudanarwa a Makarantar sakandare dake kan titin Makarfi a Gundumar Rigasa Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar (RAAF) Ismail muhammad, ya bayyana cewa wannan wani babban Kalubale ne da yake ci musu tuwo a kwarya ganin irin yadda manyan yankin suka zura musu ido a kan ganin cewa sun cimma burinsu na samun damar cike gurbin da hukumar zabe ta basu na karin akwatunan zabe a Gundumar.

Ya ce “wannan wata babbar dama ce da hukumar zaben ta bamu na karin akwatunan, kuma wani aiki ne wanda muka saka kanmu a kan yin shi wanda a sanadiyarsa hakan mafi yawanmu bama ko zuwa aiki domin mu samu ganin cewa mun cimma burin mu ta yadda mutanen mu na Gundumar Rigasa zasu cike wannan gurbin na damar da aka samu.”

“Allah Ya horewa Gundumar Rigasa mutane masu yawan gaske wanda inda zamu samu irin goyon bayan da muke bukata na karin na’urar tantancewa daga hukumar zabe, kana da wasu mutanen da zasu taimakawa aikin yin katin Zaben a Gundumar, toh da ba shakka zamu samu biyan bukatar da ake nema na samun koda mazabar da za a iya bamu Dan Majalisa ne yanzu ba lalle sai mun yi tunanin samun karamar hukuma ba.”

“Ada muna da akwatinan zabe 26 amma a yanzu an kara mana akwatuna 127 su ka zama 153, kuma a iya kokarinmu mun samu kewayawa sama da akwatina 80, toh amma idan ba a samu mutanen da suka Kada Kuri’unsu a wajejen ba a lokacin Zabe, toh ba shakka za a soke mana wadannan akwatunan don haka muke kira ga duka Jama’ar Gundumar Rigasa dasu rungumi wannan aikin zaben gadan-gadan domin ganin mun raya wadannan akwatunan.”

“Mu ba damuwarmu bane idan har mutum ya yi katin zaben yazo ranar zaben ya dangwada duk abin da yake so koda lalata Kuri’arsu za suyi, muddun idan har zai zamana za a iya lissafawa da Kuri’ar ta su wanda hakan zai nuna cewa akwai masu yin zabe a akwatunan, don ba muna yin aikin domin wani dan siyasa ko Jam’iyya ba ne, face sai don ganin ci gaban Gundumar ta mu.” Inji Shi

Acewarsa, dukda iya Kokarin da suke, wasu al’umma na zargin ko biyansu ake ko an biya su ne domin su yi wannan aikin wanda su suka daukarwa kansu yin aikin, kana da yin amfanin da karfinsu, iliminsu, basirarsu da dukiyarsu amma hakan bai hana a ci musu mutunci a wajen wasu al’ummar ayayin da suke gudanar da ayyukan katin zaben.

Shugaban RAAF, ya ci gaba da cewa su babban burin su shi ne duk wasu masu zuwa wajen garin Rigasa yin zabe da su dawo da katinansu cikin Gundumar, sannan duk wasu masu matsala a katinsu da su yi kokarin zuwa su gyara saboda amfanin kansu da kuma ci gaban duka al’ummar yankin.

A karshe, Ismail muhammad ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, masu hali, masu hannu da shuni da yan siyasar dake Gundumar da su kawo musu agaji da taimako wajen ganin yankin ta samu damar cin gashin kanta ta hanyar samun nasara a wannan aikin katin zaben wanda a halin yanzu ake bukatar agaji na gaugawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here