Mazabu 11 Sun Yabawa Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa

0
372

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SHUGABAN Karamar hukumar Dawakin Tofa Alhaji Ado Tambai Kwa ya Sami yabo daga al’ummar yankin dake mazabu 11 saboda kokarin da yake yi wajen kyautata rayuwar al’umma tare da samar da aiyukan alheri ga kowane sashe bisa la’akari da bukatun kowane bangare.

A wata ganawa da wakilin mu ya yi da wasu al’umomin yankin, sun sanar da cewa majalisar Karamar hukumar Dawakin Tofa tana kokari sosai wajen assassa wasu aiyuka wanda gwamnatin jiha ke aiwatar wa sannan tana gudanar da nata aiuykan bisa jagorancin zababben Shugaban Karamar hukumar watau Alhaji Ado Tambai Kwa.

Haka kuma, dukkanin wadanda suka yi magana da wakilin namu, sun nunar da cewa Alhaji Ado Tambai shugaba ne nagari Wanda Kuma yake baiwa kowa kulawa muddin dai an je gareshi Wanda hakan ta sanya dukkanin mazabu 11 suke jinjinawa masa bisa wannan Kokari da gwamnatin sa keyi.

Malam Umar Abubakar Dan Amar daga mazabar Gargari ya ce ” wajibi ne al’ummar karamar hukumar Dawakin Tofa su yabawa Alhaji Ado Tambai Kwa saboda yadda gwamnatin sa take Kokari duk da karancin kudade hannun kananan hukumomi wajen samar da aiyukan alheri ga al’umma ba tare da nuna gajiyawa ba”.

Shima a nasa tsokacin, Malam Sunusi Gwaida daga mazabar Marke ya bayyana shugaba Ado Tambai kwa a matsayin jagora na gaskiya wanda kuma yake da kaifin basirar tafiyar da shugabanci bisa amana da adalci ta yadda za a ci gaba da amfanar jagorancin sa.

A karshe dukanin mutanen da suka yi bayanai kan shugaba Ado Tambai sun nuna gamsarwa da yadda Karamar hukumar Dawakin Tofa take alkinta abin dake hannu wajen yiwa al’umma aiyuka a dukkanin mazabu 11 da ake dasu a fadin Karamar hukumar.

Leave a Reply