Rashin Halaccin PDP A Jihar Taraba Yasa Ni Canza Sheka Zuwa APC – Sanata Bwacha

0
518

Daga; Bashir Bello, Majalisa Abuja.

A BISA kokarin da suke na ganin cewa an tsabtace harkar siyasa a Jihar Taraba, wani jigon a Jam’iyyar PDP, Sanata Emmanuel Bwacha ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC sakamakon irin rashin halaccin da ‘ya’yan Jam’iyyar ke nunawa yayin gudanar da al’amura a Jihar.

Da yake zantawa da manema labarai, Bwacha ya bayyana cewa shi halastaccen dan Jam’iyyar PDP ne amma ganin irin yadda al’amura suka sauya ba tare da nuna kishin al’umma ba kuma da nuna gaba yasa ya sama wa kansa sauki ta hanyar canza sheka izuwa Jam’iyyar APC.

Ya kara da cewa, dalilin da yasa ya bar Jam’iyyar PDP kamar yadda ya saba yin bayanai a yan kwanakin da suka gabata, dole ce ta sanya shi domin bai taba barin Jam’iyyar PDP ba, bai taba canza sheka ba daga PDP tun akalla shekaru 25 da na shige ta.

Ya ce “Dalilin da yasa na canza Jam’iyya na koma APC shi ne, a yanzu ba PDP da na sani bace wanda muka kafa, musamman a Jihar Taraba, yanzu PDP na da
shugabancin da ba don taimakon al’umma take yi ba, sai don son zuciya da shugabanci irin na fir’una wanda idan mutum ya tashi nuna maka wariya, sai ya ce yana maka na kyashi ne domin ya ga kana yi wa al’umma abubuwa masu kyau, domin kai kana kawo wa al’umma ayyuka dake faranta zukatansu.”

“Sai kaga shugaba na maka kyashi, yana maka kiyayya a sarari, idan ya zamana za ka Kaddamar da wasu ayyukan, duka wanda ke cikin Gwamnatin sai kaga sun ki zuwa wajen wanda abinda su basu iya yi ba a matsayin su wani na yi, amadadin kai kawai ka ce masa ka gode don yana sauke maka wani dawainiya, amma sai kaga mutum yana Kawo kishi da kiyayya.”

“Naga wannan yana Kawo banbance banbance tsakanina da magoya bayana dana Gwamna shi ne nace toh gara na tashi domin akwai rabe-raben kai, wanda har hakan ya kawo lokacin da aka shirya taron shugabancin Jam’iyyar ba a sanar da ni, bayan ba wani shugaban mazaba na Jam’iyyata ta PDP da bansan shi ba, domin wannan shi ne Jam’iyyar da nayi komai domin na tabbatar ya zauna a matakin Jaha.”

“Mu muka kawo Jam’iyyar mu ka yi wahalar da muka kafa tun lokacin Solomon har zuwa yau, toh sai wani kawai ya fito ba daga inda muka san shi ba yazo ya shiga don ya yi amfani da mu saboda ganin biyayya da muke da shi ga manyan mu suka ce mu Zabe shi, iyayen mu suka ce mu Zabe shi kuma muka Zabe shi, amma kawai sai muka zo muka gane cewa wannan mutumin karara ne muka zuba a kan mu wanda a yanzu halin da muke ciki, bama iya motsi, shi yasa yanzu gara na je na fake a wani waje na samu iska da yanci na kaina inyi siyasa na hankali Kwance.”

Acewarsa, tuntuni mutane al’ummarsa sun kwana biyu suna jiran ya fita daga PDP tun da jimawa tun kamin zaben da ya gabata na zaben 2019, kuma dalilin kuwa shi ne sun gane cewa Gwamnan Jihar na Kokarin ya fadi zaben shi yasa suka ce ya fita ya je ya canza wannan Jam’iyyar ta PDPamma yace zai tsaya.

Emmanuel Bwacha ya ci gaba da cewa, Gwamnan ya kawo Kwamishinan Kudi na Jihar ya tsaya takara da shi, amma da ya fadi sai ya koma ya sake mayar da shi bakin aikinsa, hakan yasa ya kawo wani daga Jam’iyyar APGA ya bashi damin Kudi da wani tsohon Sanata kuma tsohon minista, amma suka ka dashi don bai ma zo na biyu ba saboda Jam’iyyar APC ce ta biyu amma shi yazo na karshe yayinda shi yaci zaben.

Hakazalika, tun daga wannan lokacin ba zaman lafiya a tsakanin su amma yana hadiyewa ne da hakura, domin littafi mai tsarki ya nuna musu cewa suyi addu’a, toh amma yayi addu’ar yaga ba canji saboda idan kana hulda da mutumin da zuciyar shi kaman na Dutse take, kuma ya koma gefen iblis dole ka fita harkar shi.

“Lokacin da aka yi taron da ya fitar shugabannin wannan Jam’iyyar ta PDP, bai tuntube ni ba, yace duk wanda ya neme ni ya nemi shawara ta za a kore shi daga Jam’iyyar, kuma bansan waye shugaban Jam’iyyar na mazaba ta ba kuma ni mamba ne na manyan Jami’ai (NEC) na Jam’iyyar a matakin Kasa, sai naga shi ma baya bani hakkina kamar ko yana tsoron Gwamna ne ko ya bashi cin hanci ne, don haka naga gara na fita harkar su naje Inda mutuncina zai kasance a tsare, kuma zan zauna cikin lumana.”

“Halin da muke ciki a Jihar Taraba, kowa ya gaji, kowa yana kuka, shi yasa yanzu a ko wani irin Jam’iyya idan za a samu mutumin da zai yi adalci, za a kada wannan Gwamnatin Jihar balle ma a Jam’iyyar APC da take zuwa na biyu, kuma APC na da mutane a kasa, hakan yasa Kada Gwamnatin Jihar a lokacin Zabe ba zai zama matsala ba.”

“Ba ni da matsala da su. Kuma ku tuna, duk wani harka da za kuyi, kar kuyi zaton kowa zai so ku. Ba a rasa wadansu kalilan wadanda suke ganin a’a, saboda da an barni anan ne zai tsaya takara koda ba zai ci don ace za a iya bashi matsayin Minista, toh da akwai duk irin wadannan mun san da su amma mu muna so mu tsaya takara ne don mu ci, ba wai don sunan an tsaya Zabe ba, saboda haka irin wadannan suna nan sun tsaya a gefe da bakin ciki, kuma ta yiyu sune suke tura wadansu kalilan mutane suna Zage-zage, toh duk munsan da su amma duk ba zai dame mu ba domin burinmu shi ne mu ci Zabe kawai kuma idan Allah Ya yarda zamu ci.” Inji Shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here