Daga; Isah Ahmed, Jos.
DAN majalisar wakilai ta tarayya, mai wakilyar Mazabar Lere da ke Jihar Kaduna, Injiniya Ahmed Mannur, ya baiwa wata yarinya ‘yar shekara 13 da haihuwa, mai suna Sumayya Idris da ke zaune a garin Saminaka, kyautar mota kirar Fijo 406, aboda ta zama ta biyu a gasar karatun Alkura’ani mai girma ta Jihar Kaduna da aka gudanar. Ita dai Sumayya Idris, tazo ta biyu ne a gasar karatun Alkura’ani Izu biyu da aka gudanar.
Da yake mika wannan kyautar mota ga Shugaban kwamitin shirya gasar karatun Alkura’ani na Karamar Hukumar Lere kuma Limamin masallacin Juma’a na Kamfa da ke garin Saminaka Imam Aminu Muhammad Aminu da iyayen wannan yarinya, a garin Saminaka, Mai taimakawa Dan majalisar wakilan na musamman Barista Nuhu A.Nuhu ya bayyana cewa, Dan majalisar wakilai ta tarayya Injiniya Ahmed Mannur ne, ya wakilta shi, don ya zo ya mikawa Sumayya Idris alkawarin da ya yi, na kyautar mota. Saboda nasarar da ta samu na kasancewa ta biyu a gasar karatun Alkura’ani ta jihar Kaduna a matakin Izu na biyu.
“Ganin wannan kokari da tayi, yasa ya yi mata alkawarin kyautar mota kirar fijo 406 ,kuma yau gashi ya aiko da wannan alkawari da ya yi. Muna kira ga yara matasa na wannan mazaba, su kara kokari domin wannan kyauta da ya yiwa wannan yarinya, ya fara ne ga dukkan matasan wannan yanki, musamman masu kokari”.
Da yake jawabi Shugaban kwamitin shirya gasar karatun Alkura’ani na Karamar Hukumar Lere, Imam Aminu Muhammad Aminu ya bayyana matukar farin cikin su, da godiyarsu ga wannan Dan majalisa.
Ya ce wannan karramawa da wannan dan majalisa ya yi masu, wani babban girmama ne, kuma duk mutumin da ya girmama ma’abucin ilmi, ya girmama ilmin ne.
Ya yi kira ga ‘yan majalisa da sauran masu hanu da shuni, su yi koyi da wannan dan majalisa.
Da take zantawa da wakilinmu, Sumayya Idris ta bayyana cewa gaskiya
lokacin da aka ce tazo ta biyu a wannan gasa, sai taji kamar tana mafarki ne.
Ta ce tayi farin ciki da wannan kyautar mota da aka bata, don haka tayi godiya tare da rokon Allah ya sakawa, wannan dan majalisa da alheri.