Daga; Isah Ahmed, Jos.
CIBIYAR koyawa mata sana’o’i ta Memxee, da ke garin Jos babban birnin jihar Filato, ta yi bikin yaye dalibai mata guda 120, da ta koyawa sana’o’in man shafawa da girke girke da zanin gado da fulillika da dinkin kaya da gyaran gashi da dai sauransu, a karshen makon nan da ya gabata.
Da take jawabi a wajen, Barista Mariya Mohammed Shittu ta bayyana cewa
babu shakka, wadda ta kafa wannan cibiya ta Memxee ta taimakawa mata, don haka dole a yaba mata, a karfafa mata gwiwa kan wannan kokari da tayi.
Ta ce zamani ya wuce da mace zata tsaya, sai mijinta ya yi mata komai na dawainiyar gida.
“Duk macen da ta koyi sana’a zata taimaki kanta da iyalanta. Don haka, kada ku yi wasa da wadannan sana’o’i da kuka koya. Ku dauki wadannan sana’o’i da mahimmanci.Ku taimaki kanku, ku taimaki al’umma baki daya”.
Itama a nata jawabin, Malama Ummul Khari Iliyasu ta bayyana cewa
yanzu maza da dama basa sayawa matansu kayan kwalliya. Don haka suke tsufa da wuri.
Ta yi kira ga wadannan mata su rike wadannan sana’o’i da aka koya masu, don su dugara da kansu.
Tun da farko a nata jawabin, Shugabar wannan Cibiya ta koyawa mata sana’o’i ta Memxee, Maimuna Muhammed Bashir ta bayyana cewa, ta kafa wannan cibiya ce a lokacin da aka yi kullen cutar annobar Kwarona, ganin irin mawuyacin halin da mata suka shiga, sakamakon rashin sana’a.
“Sana’o’in da muke koyarwa a wannan cibiya sune girke girke da sabulu da man shafawa da zanin gado da fulillika da dinki. A yau mun yaye dalibai mata da muka koyawa masu wadannan sana’o’i guda 120. Kuma daga lokacin da muka buxe wannann cibiya zuwa yanzu, mun yaye mata guda 1400, da suka fito daga nan Jos da garuruwan Mista Ali da ke Karamar Hukumar Bassa da Dadin kowa da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu da Lamingo da ke Karamar Hukumar Jos ta gabas”.
Maimuna ta yi bayanin cewa, babban burinsu shi ne su ga cewa kowace mace, ta koyi sana’a kuma ta dogara da kanta.