Fulani Makiyaya sun koka  a kai musu ɗauki a Kudancin Najeriya

1
844

f

Daga Rabo Haladu 

Wasu al’ummar Fulani Makiyaya da aka kora daga garin Igangan na jihar Oyo a bara, da yanzu haka ke gudun hijira a wasu wuraren na kukan neman taimako.

Makiyayan sun ce har yanzu suna cikin mawuyacin hali, kuma babu wani tallafi da aka kai musu.

Al’amarin dai ya tilasta wa da dama daga cikinsu yin barace-barace don samun abin da za su ci.

A watan Janairun shekarar da ta gabata ne aka kai wa Fulanin harin a rugagensu tare da kashe wasunsu da dabbobinsu da kona masu gidaje.S

Shekara guda bayan harin da aka kai wa Makiyayan, a Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa a jihar Oyo, har yanzu rayuwarsu tana cikin babbar matsala, a cewar Aliyu Dan Sarkin Fulanin jihar Oyo.

Ya ce har yanzu ba su da takamaiman wuri guda na zama, ‘ya’yansu ba sa zuwa makarantar boko, babu makarantar allo wasu kafin su samu abinci matsala ce, wasu ma tun da aka yi abin, ba a san inda suke ba.

“Sana’o’in da muke yi a baya babu wadanda ba su da makwanci, amma a yanzu a masallaci mu ke kwana, wasu sai sun yi bara sannan suke samun abin kai wa bakin salati,” in ji shi.

Dan Sarkin Fulanin na jihar Oyo ya kara da cewa, duk da wannan hali da suke ciki, har yanzu ba wani labarin tallafi da zai rage masu radadi matsanancin halin ƙunci da suka tsinci kan su.

Ya ce an kai mana wannan hari ne babu shiri an tarwatsa rayuwar wadanda, ba su ji ba, ba su gani ba.

1 COMMENT

Leave a Reply