Matashi a garin Gashuwa ta jihar Yobe, mai suna Umar Aminu Ahmad, wanda aka fi sani da Umar Ɗan Paleti, ya ɗauki buhun shinkafa a kansa, mai nauyin kilogram 100 inda ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, don ya ci gasar wayar Android da suka yi.
Wannan lamari ya faru ne a jiya Jumu’a, a unguwar Tsamiya, Zangon Takari. Inda matasan suka yi gasa a kan duk wanda ya ɗauki buhun shinkafa mai nauyin kilogram 100, daga Zangon Takari zuwa Kara (sabuwar kasuwar ‘yan shinkafa), a cikin garin Gashuwa, to zai ba da wayarsa ta Android. Nan take Umar ya ce zai iya, shi ma Umar ya saka wayarsa, a kan idan bai kai ba, shi ma ya ba da wayarsa.
Ku kuma karanta: Katin shedar ɗan ƙasa ya fallasa kwamandojin Boko Haram 7 da suka dawo daga aikin Hajji – Minista
Aka ɗauko buhun shinkafa aka ɗora masa, tun daga Zangon Takari, har zuwa Kara, Umar ya kawo buhun shinkafar nan bai tsaya ba. Nan take aka ba shi waya ƙirar Android da aka yi gasa akai.


A wani faifayin ‘video’ da Neptune Prime ta samu, wanda Assalafy Multimedia take tattauna wa Umar ɗin, ya tabbatar da cewa lallai ya ɗauki buhun shinkafa ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, bisa gasa da suka yi a tsakanin su, kuma ya ci wayar Android.
Da ake tambayarsa, kan cewa bayan wayar Android an ba shi dubu 100, sai Umar yace “Ni ba wanda ya ba ni dubu 100. Iya waya ce muka yi gasa a kanta, kuma ita aka ba ni. Sai dai a hanya ta tafiya, mutane sun yi ta jinjina min, wasu suna ba ni kuɗi, kuma hakan shi ne ya ƙara min ƙarfin gwiwa da kuzari har na yi nasara a wannan gasar.
“Lallai ni ban taɓa yin sana’ar dako ba, kawai dai na ga zan iya ne, shi ya sa na yi” inji Umar


