HARSHEN HAUSA A ZAMANIN FASAHAR AI
Daga Yusuf Lawan Nasidi
A da, samun wasu ayyukan fasaha na buƙatar lokaci da kuɗi da kuma neman ƙwararrun mutane. Idan mutum yana son rubuta littafi, ko ya yi zane, ko ya shirya gabatarwa, ko ya fassara wani abu zuwa wani harshe ko ya samar da bidiyo, sau da yawa sai ya nemi wanda ya ƙware a waɗannan fannoni. Amma a yau, fasahar AI (Artificial Intelligence), wato basirar na’ura, ta kawo sauyi mai yawa. Abin da a da sai an yi tafiya ko an kashe kuɗi mai yawa kafin a samu, a yanzu ana iya aiwatar da shi cikin ‘yan mintuna ƙalilan ta hanyar amfani da wayar hannu ko kwamfuta. Wannan na daga cikin manyan sauye-sauyen da duniya ke samu a wannan zamani.
Wannan ci gaba ya zo da wata babbar dama ga Hausawa da harshensu. Hausa na daga cikin harsunan Afirka da fasahohin AI suka fara tallafawa, duk da cewa har yanzu akwai sauran “rina a kaba”, kafin a kai ga cikakkiyar fahimta da ƙwarewa a dukkan fannoni. Wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne, musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu harsunan Afirka ke fuskantar ƙalubalen samun isassun bayanai da rubuce-rubuce a intanet domin bunƙasa harshen su a fannin fasahar zamani.
A yau, masu amfani da harshen Hausa za su iya amfani da AI wajen rubuta wasiƙa ko maƙala ko labari ko shirya gabatarwa ta PowerPoint domin makaranta ko wajen aiki. Za su iya neman a yi musu zane domin kasuwanci, a samar musu da tallace-tallace ko a gyara musu rubutu ko ayi fassara daga Hausa zuwa Turanci ko kuma daga Turanci zuwa Hausa, har ma da wasu harsunan. Manoma ko ɗalibai ko malamai ko ‘yan kasuwa ko marubuta ko ma’aikata duk za su iya cin moriyar wannan fasahar gwargwadon buƙatunsu.
Akwai kayan aikin AI da dama da ake iya amfani da su wajen mu’amala da Hausa a yau. Daga cikinsu akwai Meta AI wanda ake samu a WhatsApp da Facebook da ChatGPT da Microsoft Copilot da Google Gemini da sauransu. Haka kuma, Google Translate yana taimakawa wajen fassara Hausa zuwa wasu harsuna da akasin haka. Waɗannan fasahohi sun ƙara buɗe wata sabuwar kafa ga Hausawa da kuma masu amfani da harshen Hausa wajen sadarwa da za su iya amfani da ita wajen isar da harshensu da al’adunsu ga duniya.
Wannan yana nufin Hausa ba ta tsaya a cikin gida ko yankunan da ake magana da ita kawai ba. Ta samu wata sabuwar kafa ta shiga duniyar sadarwa da fasaha, inda mutane daga sassa daban-daban na duniya za su iya neman bayanai game da harshen ko al’adun Hausawa ko tarihin al’ummar Hausawa da sauran abubuwan da suka shafe su.
Amfanin wannan ci gaba yana da yawa. Na farko, zai taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar darussa da koyon karatu da rubutu. Ɗalibi zai iya neman a yi masa bayani kan wani darasi da Hausa, sannan ya fahimci abin da zai taimaka masa wajen karatunsa. Na biyu, zai taimaka wa ‘yan kasuwa wajen tallata hajojinsu ga mutane daga wurare daban-daban. Na uku, zai taimaka wa marubuta da ‘yan jarida wajen gudanar da bincike da gyara rubuce-rubucensu domin isar da saƙonni ga jama’a a cikin sauƙi.
Haka kuma, AI na iya taka muhimmiyar rawa wajen adana al’adun Hausawa, kamar abin da ya shafi Karin magana da tatsuniya da waƙa da kirari da yabo da habaici da ma labaran da kakanninmu suka gada, za a iya tattara su, a rubuta a adana ta hanyar fasahar zamani. Idan aka yi wannan aiki yadda ya kamata, al’ummomi masu zuwa za su samu damar karanta waɗannan abubuwa, su fahimce su, su kuma ci gaba da amfani da su. Wannan wata dama ce da bai kamata mu yi wasa da ita ba.
Sai dai, duk da wannan babbar dama, akwai ƙalubalen da ya kamata mu fahimta. Ba komai ne AI yake fahimta ba, shi ma yana iya yin kurakurai. Wani lokaci yana iya fassara kalma ba daidai ba, ya karkatar da ma’anar karin magana, ko ya kasa fahimtar wasu kalmomi da salon magana na musamman a Hausa. Haka kuma, yana iya samar da bayanai da ba su da cikakkun sahihanci. Saboda haka, bai kamata mu ɗauki duk abin da AI ya bayar a matsayin gaskiya ba. Ya kamata marubuta da malamai da masana da manazarta harshe su riƙa tantancewa da gyara bayanan da AI yake bayarwa.
A nan ne rawar da Hausawa za su taka ta fi muhimmanci. Bai kamata mu tsaya kawai ga amfani da AI wajen amsa tambayoyi ko samar da rubuce-rubuce ba. Ya kamata mu ƙara samar da ingantattun rubuce-rubuce na Hausa a intanet, mu tattara littattafai da kundin kalmomi da karin magana da tatsuniyoyi da sauran taskokin harshenmu. Masana harshe, malamai, marubuta da masu bincike su haɗa kai wajen tabbatar da cewa Hausa ta samu gata da matsayi mai girma a duniyar fasahar zamani.
Ya kamata mu riƙa amfani da Hausa wajen yin tambayoyi ga AI, mu gyara masa idan ya yi kuskure, mu kuma ƙara samar da bayanai masu inganci da za su taimaka wajen bunƙasa harshen. Hakan zai taimaka wajen ƙara yawan bayanan Hausa da ake samu a duniyar fasaha, tare da inganta yadda waɗannan na’urori ke fahimtar harshenmu.
A ƙarshe, makomar Hausa a duniyar fasahar AI ba za ta dogara da kamfanonin fasaha kaɗai ba. Tana hannunmu, watau Hausawa da masu amfani da harshen Hausa. Idan muka yi watsi da wannan dama, za mu iya barin wasu su tsara mana makomar harshenmu ba tare da gudummawarmu ba. Amma idan muka rungumi fasahar, muka samar da bayanai masu inganci, muka kuma yi amfani da ita wajen bunƙasa harshenmu, Hausa za ta samu matsayi mafi girma a duniyar fasaha.
AI ya buɗe mana ƙofa. Abin da ya rage shi ne mu shiga cikinta, mu tabbatar da cewa harshen Hausa bai tsaya a bayan fage ba a wannan sabon zamani na fasaha.
Yusuf Lawan Nasidi ya rubuta daga Unguwar Hausawa Asibiti, Potiskum, Jihar Yobe. Ana iya tuntuɓarsa ta adireshin imel: nasidi30@gmail.com.


