Gwamnan Katsina Ya je Ta’aziyya Ga iyalan Marigayi Sheikh Masussuka
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa gidan iyalan marigayi Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma, domin yi musu ta’aziyya bayan kisan da aka yi wa malamin.
Tsohon gwamnan jihar, Barrister Ibrahim Shehu Shema, da iyalan marigayin ne suka tarbi gwamnan da tawagarsa.
Radda ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga iyalansa, al’ummar Musulmi da Jihar Katsina baki ɗaya. Ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya karɓi ayyukansa na alheri, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdausi.
Zaɓen 2027: Ba za mu janye wa Atiku ba – Kwankwaso

Kwamishinan Harkokin Addini na jihar, Hon. Ishaq Shehu Dabai, ya miƙa ta’aziyyar gwamnati da al’ummar jihar, tare da roƙon Allah Ya ba iyalan marigayin haƙuri da juriya.
Yadda Ake Tantance (Verifying) Facebook Account Da Facebook Page
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya saka wa marigayin da alheri bisa gudummawar da ya bayar wajen koyar da addinin Musulunci da zaman lafiya.


