Ronaldo Zai Yi Bankwana da Taka Leda
Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Portugal, kuma Shugaban duk ‘yan wasan Duniya Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa akwai yiwuwar wannan shekarar ta zama shekararsa ta ƙarshe yana taka leda a matsayin ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa.
Ronaldo ya ce ya riga ya tsara rayuwarsa gaba ɗaya bayan kammala harkar ƙwallon ƙafa, yana mai cewa yana da wasu muhimman abubuwa da yake son mayar da hankali a kansu.«“Wataƙila wannan ne shekarata ta ƙarshe a matsayin ɗan wasan ƙwallon ƙafa.
Na tsara makomata gaba ɗaya, kuma hakan yana da matuƙar muhimmanci a gare ni,” in ji Ronaldo.»Ya bayyana cewa bayan ƙwallon ƙafa, zai samu abubuwa da dama da za su shagaltar da shi, domin gudun kada ya fuskanci babban gibi da ka iya tasowa bayan barin wasan da ya shafe shekaru yana yi.
Ku kuma karanta: Muna kare ku daga Rasha, amma kun ƙi taimaka mana kan Iran – Trump ga Turai
Ronaldo ya ce yana shirin ƙara yin tafiye-tafiye, jin daɗin rayuwa, da kuma kallon da buga wasan padel, wanda ya ce yana matuƙar kauna.
Ya ƙara da cewa yana son ci gaba da more abubuwan da ya samu sakamakon shekaru masu yawa na aiki da sadaukarwa.“Domin shekaru 25 sun kasance shekaru cike da sadaukarwa a kowace rana,” in ji Ronaldo.
Maganganun fitaccen ɗan wasan sun sake tayar da hankalin masoyan ƙwallon ƙafa a duniya, musamman ganin cewa Ronaldo ya shafe kusan shekaru 25 yana kan gaba wajen haskawa a fagen ƙwallon ƙafa.
Idan har ya tabbatar da yin ritaya, hakan zai kasance ƙarshen wani gagarumin zamani a tarihin ƙwallon ƙafa, bayan Ronaldo ya kafa tarihi da dama tare da lashe kofuna da lambobin yabo masu yawa a tsawon rayuwarsa.Ga alama, ranar bankwana da filin wasa tana ƙara kusantowa.


