Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeAddiniCikin Ruwan Sama,...

Cikin Ruwan Sama, Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin Annabi (SAWW) a Potiskum

Cikin Ruwan Sama, Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin Annabi Muhammad (SAWW) a Potiskum

Cikin mamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, ɗaruruwan al’ummar musulmi haɗe da makarantun Islamiyyoyi sama da 700 ne suka fito zagayen Mauludin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAWW) a garin Potiskum jihar Yobe.

Shi dai irin wannan zagayen Mauludin ana gudanar da shi ne a kowace Asabar ɗin farko na watan Rabi’ul Awwal na kowace shekara.

Makarantun Islamiyyoyi suna taruwa ne a ƙofar fadar mai martaba Sarkin Fika da ke Potiskum, daga nan sai a shiga sahu cikin tsari ana zagaye cikin gari, yayin da Sarkin ke zaune yana kallon masu wucewa.

A lokacin zagayen Mauludin, ana zagaye kusan dukkan manyan titunan cikin garin Potiskum. Garin Potiskum ya tsaya cak, saboda cincirindon masu zagayen Mauludin.

Ku kuma karanta: ‘Yar shekaru 24, ta zama ɗaliba ta farko da ta kammala karatun Digiri a fannin Shari’a da sakamako mafi daraja

Ɗaliban Fudiyya da Harisawa suna tafe cikin sahu suna taka faretin girmamawa ga Manzon Allah (SAWW), yayin da ɗimbim al’umma suka yi cincirindon suna kallon su.

A cikin masu zagayen Mauludin na Annabi Muhammad (SAWW), akwai waɗanda suka yi shigar wasu daga cikin ƙabilun ƙasar nan;

  1. Ibo
  2. Yoruba
  3. Kanuri
  4. Fulani
  5. Bolawa
  6. Ngizim
  7. Kare-Kare
    Da sauransu.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

BIZ Sister Kano Ta Gudanar da Taron Ƙarfafa Mata Kan Harkokin Kasuwanci

BIZ Sister Kano Ta Gudanar da Taron Ƙarfafa Mata Kan Harkokin Kasuwanci Daga Shafaatu Dauda Kano Ƙungiyar Matasan Mata ‘Yan Kasuwa reshen Jihar Kano, BIZ Sister Kano, ta gudanar da wani taron ƙara wa juna sani da ƙarfafa gwiwa kan harkokin...

Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya

Al’ummar Unguwar Kurna da ke Kano Sun Koka Kan Rashin Hanya Daga Shafaatu Dauda Mazauna yankin Anguwar Kurna Karshen Kwalta zuwa Kurna Tudu dake Karamar Hukumar Ungogo ta jihar Kano sun koka kan rashin kyakkyawar hanyar mota, inda suka ce matsalar...

Yadda aka yi bikin al’adu na ABUSRC a ABU Zariya

Yadda aka yi bikin al’adu na ABUSRC a ABU Zariya Daga Idris Umar, Zariya Majalisar Wakilan Ɗalibai ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABUSRC) ta fara bikin al’adunta, inda aka fara da gasar girke-girke tsakanin ɗalibai daga jihohi da kabilu daban-daban. An gudanar da...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.