An yi wa wata fitacciyar mawaƙiya haɗe da mutane huɗu daga tawagarta bulala a Jamhuriyar Musulunci ta Iran saboda wani wasa da suka gabatar ba tare da ta sanya hijabi ba, in ji lauyoyinsu.
Lauyoyin nasu sun shaida wa BBC cewa an yi wa Parastoo Ahmadi, da mawaƙa uku da wani furodusa bulala 74 kowannensu a birnin Qom.
Ahmadi mai shekara 29 ta fito sanye da riga marar hannu a wani wasa da aka watsa kai tsaye ta intanet a watan Disamban 2024. Dokokin Iran sun haramta wa mata yin wasa a bainar jama’a tare da wajabta musu sanya hijabi.
A watan Yunin da ya gabata, wata kotu a Qom ta same ta da wasu mutum takwas da laifin “saɓa tarbiyyar jama’a” ta hanyar wallafa “abubuwan da ba su dace ba kuma na rashin ɗa’a”.
Baya ga hukuncin bulala 74 da aka yi musu, an kuma hana su gudanar da ayyukan sauti da bidiyo tare da hana su fita ƙasar na tsawon shekara biyu.
Ku Kuma Karanta: Yaƙin Iran ne ya janyo wa jam’iyyarmu rashin nasara – Trump
Lauyoyinsu sun ce a ƙarshen watan Satumba, wata kotun ɗaukaka ƙara a Qom ta yi watsi da ƙarar da waɗanda aka hukunta suka shigar, tare da tabbatar da hukuncin da aka yanke musu.
Hukuncin ya jawo suka daga wasu masu rajin kare haƙƙin bil’adama a Iran, waɗanda suka ce hukuncin bulala azabtarwa ce mai tsauri da wulaƙanci, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da ke haramta azabtarwa.
A ranar Litinin, ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda aka hukunta ya shaida wa BBC cewa an yi wa Ahmadi da wasu maza huɗu da ake tuhuma tare da ita bulala a reshe na uku na ofishin aiwatar da hukuncin laifuffuka da ke birnin Qom.


