Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

OECD 2024 raporuna göre, Avrupa’daki lisanssız bahis sitelerinin oranı %35’tir; bu, bettilt giriş gibi lisanslı sitelerin önemini artırır.

bahsegel bahsegel giriş bahsegel bettilt bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş bahsegel giriş paribahis

Dijital ortamda oyun keyfini artıran https://paribahis-resmi.ink/ kategorileri öne çıkıyor.

bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bahsegel güncel giriş bettilt bettilt güncel giriş
HomeLabariYa Kamata Dandalin...

Ya Kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci Ya Zurfafa Tunani da Ƙwarewa Wajen Haɓaka Harkokin Isar da Saƙo — Dr. Hassan Gimba

Ya Kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci Ya Zurfafa Tunani da Ƙwarewa Wajen Haɓaka Harkokin Isar da Saƙo — Dr. Hassan Gimba

Taron Makon Yaɗa Labaran Harkar Musulunci, wanda ke gudana da taken “Ƙarfafa Ƙwarewar Yaɗa Labarai Domin Isar da Saƙon Harkar Musulunci Cikin Inganci”, ya shiga rana ta biyu a yau Asabar, 11 ga Jimada Sani, 1448H, daidai da 21 ga Nuwamba, 2026, a birnin Abuja.

Bayan kammala sallah da cin abinci, an ci gaba da gudanar da zaman taron, inda aka gabatar da Dr. Hassan Gimba mamallakin jaridar Neptune Prime, wanda ya gabatar da maƙala mai taken: “Tasirin Gidajen Jaridu Wajen Sauya Tunanin Al’umma”.

Ku kuma karanta: Fatima Barnawi Bafalasdiniya Yar Gwagwarmaya Yar Asalin Najeriya

A farkon jawabinsa, Dr. Gimba ya bayyana yadda suka sha gwagwarmaya a farkon-farkon da’awa wajen isar da saƙonni, duk da ƙalubale da barazanar rasa rayuwa da suka fuskanta.

Ya ci gaba da bayanin yadda aka yi amfani da jaridu wajen sauya tunanin al’umma da fahimtar kiran da Jagora Shaikh Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H) yake yi.

“A farkon-farkon gwagwarmaya, an yi amfani da jaridu wajen sauya tunanin al’umma kan hadafin Da’awar Harkar Musulunci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, bai kamata ’yan’uwa su bari mutanen gari ne kawai suke bayyana wa duniya ko su waye ba. A maimakon haka, ya kamata su kasance masu amfani da dukkan hanyoyin yaɗa labarai wajen isar da saƙonninsu ga al’umma.

Da yake magana kan muhimmancin rashin nuna wariya a aikin jarida, Dr. Gimba ya ce:

“Matsayinka na mai ba da labari, ko da kana saɓani da wani ne, ya wajaba ka faɗi gaskiya a kansa. Duk wani saƙon da kake son isarwa, ka tabbatar da cewa gaskiya ce kake bayyanawa.”

Dr. Hassan Gimba ya ba mahalarta damar yin tambayoyi, inda suka gabatar da tambayoyinsu, kuma ya amsa su nan take. Ya kuma shawarci ’yan Dandalin Yaɗa Labarai da su ƙara jajircewa wajen yin gogayya da sauran ’yan jaridu a ƙasa.

A cikin shawarwarinsa, ya jaddada cewa:

“Ya kamata Dandalin Yaɗa Labaran Harkar Musulunci ya zurfafa tunani da ƙwarewa wajen haɓaka harkokin isar da saƙon Harkar Musulunci.”

Haka kuma, a cikin jawabinsa, Dr. Gimba ya bayyana yadda aka kafa jaridar Pointer Express ta Harkar Musulunci, tare da irin gwagwarmayar da aka sha wajen yi wa jaridar rajista.

Bayan kammala jawabin Dr. Hassan Gimba, sai aka gabatar da Malam Saminu Sani, daga Liberty TV da Rediyo, inda ya gabatar da maƙalarsa mai taken: “Kafafen Yaɗa Labarai: Talabijin da Rediyo, Gudummawarsu da Muhimmancinsu Wajen Isar da Saƙo”.

A cikin jawabinsa, Malam Saminu Sani ya yi cikakken bayani kan irin gudunmawar da talabijin da gidajen rediyo suke takawa wajen isar da saƙonni ga al’umma, tare da bayyana muhimmancinsu a harkokin sadarwa. Har wala yau ya yi dogon bayani kan tarihin kafuwar rediyo da talabijin.

“Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙo,” in ji shi.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Harshen Hausa a Zamanin Fasahar AI

HARSHEN HAUSA A ZAMANIN FASAHAR AI Daga Yusuf Lawan Nasidi A da, samun wasu ayyukan fasaha na buƙatar lokaci da kuɗi da kuma neman ƙwararrun mutane. Idan mutum yana son rubuta littafi, ko ya yi zane, ko ya shirya gabatarwa, ko...

2027: Za a yi rikici a Nijeriya idan har Tinubu bai koma karo na biyu ba – Adeyemi

2027: Za a yi rikici a Nijeriya idan har Tinubu bai koma karo na biyu ba - Adeyemi Tsohon Sanatan da ya wakilci Kogi ta Yamma, Smart Adeyemi, ya yi gargaɗin cewa Najeriya na iya shiga babban rikicin siyasa idan...

Fatima Barnawi Bafalasdiniya Yar Gwagwarmaya Yar Asalin Najeriya

Fatima Barnawi Bafalasdiniya Yar Gwagwarmaya Yar Asalin Najeriya Fatima Barnawi Bafalasdiniya Yar asalin Najeriya wacce aka Haifa a Birnin Jerusalem a Falasdin. Fatima ce Mace ta farko Bafalasdiniya da ta fara Gwagwarmaya kwatar Yanci daga danniyar Yahu**dawan Isra’ila da Makami. Ita...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.