Amurka na bai wa sojojin Najeriya bayanan sirri gabanin zaɓen 2027 – Ministan Tsaro
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce Amurka na bai wa sojojin ƙasar bayanan sirri na kai-tsaye da hotunan tauraron ɗan Adam domin gano tare da kai hare-hare kan shugabannin ’yan ta’adda gabanin zaɓen 2027.
Musa ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin, inda ya ce haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya taimaka wajen inganta ayyukan sojoji, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya ce sojoji sun kashe shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda da dama a wasu hare-haren dare, tare da gudanar da kusan kullum ayyukan yaƙi da ta’addanci bisa ingantattun bayanan sirri.
Ku kuma karanta: ‘Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro:
Ministan ya kuma bayyana cewa Najeriya na sa ran samun ƙarin jiragen yaƙi masu saukar ungulu daga Amurka da Italiya domin ƙarfafa ayyukan sojojin.
Ya ce hukumomin tsaro sun ƙara shirin kare zaɓen 2027 daga tashin hankali, kafin zaɓen, lokacin gudanar da shi da kuma bayan kammalawa.
Musa ya ƙara da cewa Najeriya na sa ido kan yadda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke amfani da fasahar Starlink, kuɗaɗen intanet (cryptocurrencies) da jiragen sama marasa matuƙa wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma ce Najeriya ta cimma yarjejeniya da Kamaru, Nijar da Chadi, wadda ta bai wa sojojin ƙasashen damar bin ’yan ta’adda har zuwa kilomita biyar cikin iyakokin juna.
Ministan ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar IS-Sahel na ƙoƙarin ɗaukar ’yan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a Arewa maso Yammacin Najeriya domin mayar da su masu tsattsauran ra’ayin addini.
Ya ce akwai fargabar ’yan bindigar da a yanzu ke gudanar da ayyukansu domin kuɗi za su iya rikidewa zuwa masu tayar da ƙayar baya masu akida irin ISWAP.
Musa ya ce inganta sa ido da amfani da bayanan sirri na taimaka wa sojoji wajen gano ’yan ta’addan a cikin dazuzzuka da hana su tserewa bayan kai hare-hare.


