Matar Gwamnan Kano ta biyu kuma diyar tsohon gwamnan jihar, Zainab Musa Kwankwaso, ta shigar da karar neman kotu ta raba aurenta da Gwamna Abba Kabir Yusuf a babbar kotun yankin Gudu da ke birnin Abuja.
A cewar takardun kotun da jaridar Daily Nigerian ta samu, kotun ta aike da sammacin da ke bukatar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana a gabanta a ranar Talata 17 ga watan Nuwambar 2026 domin amsa karar.
A cikin bayanan da ta gabatar a gaban kotun, Zainab wadda suka yi aure da gwamnan a shekarar 2006 kuma suke da ‘ya’ya shida, ta bayyana cewa auren nasu ya shiga halin ni-‘yasu saboda rashin kulawa, soyayya, da kuma kwanciyar hankali.
Ta kara da cewa dukkan yunkurin sulhu da aka yi ya ci tura, don haka take neman a raba auren ta hanyar Khul’i a addinin Musulunci, tana mai bayyana cewa a shirye take ta mayar da sadakin da gwamnan ya biya a ranar daurin aurensu.
Rahoton ya ce lamarin ya biyo bayan barin gidan gwamnatin Kano da ta yi a karshen watan Oktoba zuwa gidan mahaifinta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kafin ta wuce Abuja.
Daily Nigerian ta ce ta tuntubi kwamishinan yada labarai na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa amma bai amsa kiran waya don yin karin bayani kan batun ba.


