Jikan Sheikh Nasir Kabara, Almaliky ya zo na ɗaya a gasar waƙoƙin yabon Annabi a Kano
Mawaƙi Nasir Almaliky, jikan fitaccen Malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Nasiru Kabara ya zo na farko a gasar waƙoƙin yabon Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a karon farko a Jihar Kano.
Almaliky ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya ce waƙarsa mai taken “Ma Tayssara Minal Wijdan” (ما تيسّر من الوُجدان) ce ta lashe matsayi na farko a gasar.

Ya ce an gudanar da gasar ne ƙarƙashin kulawar Cibiyar Bincike da Adana Tarihi ta Sheikh Ibrahim Niass (SIRAD), wadda Farfesa Ibrahim Maqari ke jagoranta.
A sakamakon nasarar, Almaliky ya samu babbar kyauta tare da damar zuwa aikin Umrah domin ziyartar ƙasa mai tsarki.
Ya kuma taya sauran mawaƙan da suka samu matsayi na biyu, na uku, na huɗu da na biyar murna, inda ya bayyana cewa su ma sun samu kyaututtuka da damar zuwa aikin Umrah.

Mawaƙin ya kuma yi fatan sauran waɗanda suka halarci gasar za su samu irin wannan nasara a nan gaba.
A ƙarshe, Almaliky ya gode wa dukkan waɗanda suka taya shi murna tare da yi masa fatan alheri bayan samun nasarar.


