Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara kaimi wajen ganin an kammala manyan ayyukan layukan dogo da ake gudanarwa a Arewacin Najeriya, inda ake shirin ƙaddamar da layin dogo na Kaduna zuwa Kano a ranar 3 ga Disamba, 2026.
Aikin layin dogo mai tsawon kilomita 203 na Kaduna–Zariya–Kano, wanda yana daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gada da kuma waɗanda take mayar da hankali a kansu, ya kai kusan kashi 90 cikin 100 na kammaluwa.
Haka kuma, aikin layin dogo na Kano–Katsina–Maradi, mai tsawon kilomita 400, ya kai kashi 70 cikin 100 na kammaluwa.
Idan ba a manta ba, lokacin da Shugaba Tinubu ya karɓi ragamar mulki a shekarar 2023, aikin layin dogo na Kano–Katsina–Maradi bai wuce kashi 5 cikin 100 na kammaluwa ba, yayin da na Kaduna–Kano bai kai kashi 30 cikin 100 ba.
Ku kuma karanta: Shugaba Tinubu, ya shawarci ‘yan Najeriya da su sanya idanu kan yadda gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi ke kashe kuɗaɗe
Wannan ci gaba na nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Tinubu na faɗaɗa hanyoyin sufuri na jirgin ƙasa, inganta haɗin kai tsakanin yankuna da sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji da jigilar kayayyaki a cikin Najeriya da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita.
Layin dogon na Kaduna–Kano, wanda yake ci gaban tsohon layin dogo na Abuja–Kaduna, zai samar da cikakkiyar hanyar jirgin ƙasa da za ta haɗa Abuja, Kaduna, Zariya da Kano, tare da ƙarfafa harkokin sufuri tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci na Arewacin Najeriya.
A wani mataki na tabbatar da ingancin ayyukan, wata tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, Injiniya Funso Adebiyi, ta gudanar da bincike a kan ayyukan bisa umarnin Shugaba Tinubu.
Tawagar ta nuna gamsuwa da ingancin ayyukan gine-ginen, musamman shimfiɗar layin dogo, magudanan ruwa, kariyar tuddai, shimfiɗa duwatsu da kuma matakan ƙarfafa ƙasar da aka bi domin tabbatar da ɗorewar aikin.
A yayin ziyarar, tawagar ta kuma gudanar da gwajin tafiyar jirgin ƙasa daga Jaji a Jihar Kaduna zuwa Kano, domin tantance ingancin layin dogon da aka kammala da kuma jin daɗin fasinjoji yayin tafiya.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin cewa a gaggauta warware dukkan matsalolin da suka shafi mallakar filaye da biyan diyya a cikin birnin Kaduna, domin tabbatar da kammala dukkan sassan hanyar jirgin ƙasan daga Abuja zuwa Kano.
Daga cikin ayyukan da ake shirin ƙaddamarwa a ranar 3 ga Disamba, 2026, akwai ɓangaren layin dogo mai tsawon kilomita 190 daga Jaji zuwa Kano, daga cikin jimillar kilomita 205 na aikin Kaduna–Kano.
Haka kuma, za a ƙaddamar da ɓangaren aikin Kano–Maradi mai tsawon kilomita 250, wanda ya haɗa da Dawanau, Kano, Kazaure, Daura da Katsina.
Ana sa ran da zarar layin dogo na Kaduna–Kano ya fara aiki, zai sauƙaƙa jigilar fasinjoji, bunƙasa harkokin kasuwanci tare da samar da wata hanya ta daban ga matafiya da ke amfani da manyan hanyoyin mota a ɗaya daga cikin yankunan kasuwanci mafiya muhimmanci a Arewacin Najeriya.
Haka nan, layin dogo na Kano–Katsina–Maradi, wanda ya kai kashi 70 cikin 100 na kammalawa, zai ƙara ƙarfafa zirga-zirgar sufuri da kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da buɗe sabbin damarmakin tattalin arziki ga al’ummomin da ke kan hanyar.
Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa, bisa ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za a tabbatar da kammala dukkan ayyukan samar da ababen more rayuwa da ake gudanarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan bisa jadawalin da aka tsara.
Wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na mayar da manyan ayyukan sufuri tamkar ginshiƙin bunƙasa tattalin arziki, haɗa yankuna da samar da sabbin damarmakin ci gaba ga al’ummar Najeriya.


