Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

HomeLabariNANS Shiyya ta...

NANS Shiyya ta Arewa Maso Yamma da NEARLS Sun Kulla Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Shekaru Uku

Daga Idris Umar, Zaria

Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) Shiyya ta A (Arewa maso Yamma) da National Agricultural Extension and Research Liaison Services (NEARLS) sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) ta tsawon shekaru uku domin bunƙasa kasuwancin noma, ƙarfafa ɗalibai, binciken aikin noma, tabbatar da wadatar abinci da kuma ci gaban ƙasa.

An gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a hedikwatar NEARLS da ke Ahmadu Bello University, Zariya.

A madadin NANS Shiyya ta A, Mai Kula da Shiyyar, Umar Suleiman Doko, ne ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar, a wani mataki da ke nuna ƙudirin ƙungiyar na ci gaba da samar da haɗin gwiwa masu amfani ga ɗalibai da matasa a yankin Arewa maso Yamma.

Wannan nasara ta samo asali ne daga tattaunawa da mu’amala mai ɗorewa tsakanin ɓangarorin biyu bayan wata ziyarar haɗin gwiwa da NANS ta kai wa cibiyar NEARLS a ranar 4 ga Disamba, 2025. Ziyarar ta samu jagorancin Muhammad El-Khamis, wanda a lokacin yake matsayin Daraktan Haɗin Gwiwa da Hulɗar Dabaru na NANS.

Yarjejeniyar za ta samar da tsarin haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da kasuwancin noma (Agripreneurship), binciken aikin noma, haɓaka ƙwarewar ɗalibai, damar koyon aiki a aikace, ƙarfafa matasa, shirye-shiryen tabbatar da wadatar abinci da sauran ayyukan ci gaban ƙasa.

Ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai buɗe sabbin damammaki ga ɗalibai, bunƙasa fannin noma, taimaka wa matasa su samu sana’o’i tare da rage matsalar zaman banza.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron rattaba hannu akwai Daraktan NEARLS, Yusuf Ahmad Sani, mataimakinsa Muhammad Musa Jaliya, da Ma’ajin Kudin cibiyar Komred Shehu Garba.

Sun yaba da wannan haɗin gwiwa tare da bayyana cewa zai taimaka wajen bunƙasa noma da ci gaban ƙasa.

Daraktan cibiyar ya bayyana cewa duk da ƙalubalen ƙarancin kuɗi da cibiyar ke fuskanta, za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata domin kawo ci gaba ga ƙasa baki ɗaya. Haka kuma ya jaddada aniyar cibiyar na ci gaba da bai wa ‘yan Najeriya ilimi da shawarwari a fannin noma.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara tallafa wa cibiyoyin bincike da yaɗa ilimin noma domin su samu damar faɗaɗa ayyukansu, musamman a fannin bincike, tsaron abinci da inganta rayuwar al’umma.

A ɓangaren NANS, mahalarta taron sun haɗa da Muhammad El-Khamis, Injiniya Murtala Yahuza da Abubakar Rabiu.

An rufe taron cikin nasara da kwanciyar hankali, inda mahalarta suka bayyana fatan cewa wannan yarjejeniya za ta samar da gagarumar gudunmawa ga ɗalibai, fannin noma da ci gaban Najeriya baki ɗaya.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Einsteiger im Online Casino Echtgeld: Sicher spielen und von Boni profitieren

Das Online-Casino-Erlebnis bietet unseren Spielern eine spannende und potenziell lukrative Möglichkeit, ihr Glück zu versuchen. Mit einer Vielzahl von Spielen, verlockenden Boni und sicheren Zahlungsmethoden ist es kein Wunder, dass immer mehr Menschen sich für casino online österreich Echtgeld-Casinos...

Experience massive jackpots and top slots at Dream Jackpot Casino in 2026

As 2026 unfolds, online gaming enthusiasts are in for a treat with the emergence of Dream Jackpot Casino, a platform designed to elevate the gaming experience to new heights. With a wide array of online slots, live dealer games,...

Fast Withdrawal Casino UK 2026: the ultimate choice for instant payments and reliable

Choosing a casino can be a daunting task, especially with the proliferation of online platforms offering various features. In 2026, one of the most desirable attributes for players in the UK is the speed at which they can withdraw...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.