Online bahislerde yeniliğin ve kazancın buluşma noktası bettilt olmuştur.

Adres güncellemeleriyle sorunsuz bağlantı sağlayan bettilt önemlidir.

Dijital ortamda eğlencenin en güvenilir adresi bettilt oluyor.

Bahis sektöründe kullanıcıların %61’i canlı bahisleri tercih ederken, bettilt giriş bu segmentte yüksek oranları ve hızlı işlem avantajıyla öne çıkmaktadır.

Futbol, basketbol ve daha pek çok spor dalında kupon yapmak için bahsegel bölümü tercih ediliyor.

Mobil deneyimini geliştiren bettilt sistemi oldukça popüler.

HomeGwamnatiKatin shedar ɗan...

Katin shedar ɗan ƙasa ya fallasa kwamandojin Boko Haram 7 da suka dawo daga aikin Hajji – Minista

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa tsarin tantance bayanan ’yan ƙasa na Hukumar NIMC ya taimaka wajen cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajjin 2026.

Jaridar Punch ta rawaito ministan ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar NIMC ta 2026.

A cewarsa, an kama mutanen ne a filin jirgin saman Katsina a ranar Alhamis bayan sun dawo daga Makka, sannan aka miƙa su ga Hukumar Tsaro ta DSS domin ci gaba da bincike.

Ku kuma karanta: Kotu ta soke rajistar jam’iyyar NDC

Tunji-Ojo ya ce an samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne saboda haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya tare da alaƙarsu da tsarin bayanan Interpol.

Ya bayyana cewa sabuwar dokar NIMC za ta ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar haɗa bayanan hukumomi daban-daban, tare da taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanai da sauran laifukan tsaro.

Ministan ya ƙara da cewa a baya tsarin bayanan ’yan ƙasa a Najeriya ya kasance a rarrabe, amma yanzu ba za a iya samun fasfo na Najeriya ba tare da amfani da bayanan NIMC ba.

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar NIMC ta 2026 a gaban shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu manyan jami’an gwamnati.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

Kotu a Kano ta Aike Wa Da Malam Lawan Triumph Sammaci kan Zargin Wa’azin Tunzura Jama’a

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu a Kano ta aikewa Malam Lawan Triumph sammaci domin ya bayyana a gabanta kan zargin yin kalaman da ka iya tunzura al’umma. Ku Kuma Karanta: ‘Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji...

Babban Malami a FCE Potiskum, Dakta Mamuda ya rasu, yana da shekaru 62

Babban Malami a FCE Potiskum, Dakta Mamuda ya rasu, yana da shekaru 62 Al'ummar garin Potiskum sun shiga cikin makoki da juyayi na rasuwar Dakta Abdullahi Mamuda, Babban Malami a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCET), Potiskum. Dakta Mamuda ya rasu a...

‘Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro

'Yansanda da Sojoji sun hana tsoffin Sojoji Zanga-zanga a ma’aikatar tsaro ‘Yan sanda da sojoji sun tare tsoffin jami’an tsaro da suka yi ƙoƙarin gudanar da zanga-zanga a Ma’aikatar Tsaro kan batun rashin biyan wasu kuɗaɗen gyaran fansho da suke...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.