HomeGwamnatiKatin shedar ɗan...

Katin shedar ɗan ƙasa ya fallasa kwamandojin Boko Haram 7 da suka dawo daga aikin Hajji – Minista

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa tsarin tantance bayanan ’yan ƙasa na Hukumar NIMC ya taimaka wajen cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajjin 2026.

Jaridar Punch ta rawaito ministan ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar NIMC ta 2026.

A cewarsa, an kama mutanen ne a filin jirgin saman Katsina a ranar Alhamis bayan sun dawo daga Makka, sannan aka miƙa su ga Hukumar Tsaro ta DSS domin ci gaba da bincike.

Ku kuma karanta: Kotu ta soke rajistar jam’iyyar NDC

Tunji-Ojo ya ce an samu nasarar kama waɗanda ake zargin ne saboda haɗa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya tare da alaƙarsu da tsarin bayanan Interpol.

Ya bayyana cewa sabuwar dokar NIMC za ta ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar haɗa bayanan hukumomi daban-daban, tare da taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanai da sauran laifukan tsaro.

Ministan ya ƙara da cewa a baya tsarin bayanan ’yan ƙasa a Najeriya ya kasance a rarrabe, amma yanzu ba za a iya samun fasfo na Najeriya ba tare da amfani da bayanan NIMC ba.

Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar NIMC ta 2026 a gaban shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu manyan jami’an gwamnati.

Get notified whenever we post something new!

spot_img

Create a website from scratch

Just drag and drop elements in a page to get started with Newspaper Theme.

Continue reading

A kan wayar Android, Matashi a Yobe, ya yi tafiyar kilomita 4, ɗauke da buhun shinkafa a kansa

Matashi a garin Gashuwa ta jihar Yobe, mai suna Umar Aminu Ahmad, wanda aka fi sani da Umar Ɗan Paleti, ya ɗauki buhun shinkafa a kansa, mai nauyin kilogram 100 inda ya yi tafiyar tsawon kilomita 4, don ya...

Enjoy exclusive access to all of our content

Get an online subscription and you can unlock any article you come across.